Kano Ta Dabo: Hukumar KAROTA Ta Kwace Kwalaban Giya 4,600
- Hukumar KAROTA ta yi nasarar cafke wata mota makare da kwalaben giya a kan titin Ibrahim Taiwo da ke kwaryar jihar
- KAROTA ta sha alwashin mika kwalaben giyar da suka kai 4,600 ga hukumar Hisbah don fadada bincike
- Jihar Kano na daga cikin jihohin Arewacin Najeriya da aka haramta shigowa, sayarwa da kwankwadar barasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Kano - Hukumar da ke kula da zirga-zirgar ababen hawa a jihar Kano (KAROTA) ta kwace wata mota makare da kwalaben giya 4,600 da ta shigo cikin jihar.
Mai magana da yawun hukumar, Nabilusi Kofar-Naisa, a cikin wata sanarwa ya yi nuni da cewa lokacin kamen, direban ya tsere ya bar motar a nan.
Ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Wata babbar mota mai lamba FGE 407 XB ta biyo ta titin Ibrahim Taiwo da misalin karfe 4 na yamma, inda jami'an hukumar KAROTA suka tare ta."
Daraktan hukumar KAROTA, Faisal Mahmud Kabir, ya sha alwashin mika kwalaben giyar na hukumar Hisbah don fadada bincike, rahoton jaridar Leadership.
Hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook cewa direbobin da ke shigo da giya a jihar sun fara canja dabaru, inda suke sajewa da daukar itace alhalin giya ce a kasa.
Jami'in KAROTA da ya kama motocin giya ya samu kyautar N1m
A wani labarin makamancon wannan, hukumar KAROTA ta ba wani jami'inta mai suna Halilu Jalo kyautar Naira miliyan daya bayan nasarar kama wasu motoci biyu dauke da giya a jihar.
A lokacin da Jalo ya tare motocin, an bashi cin hancin Naira dubu 500 don ya kyale motocin su wuce amma yaki karba, ya kama su, Legit ta ruwaito.
Hisbah ta farfasa kwalaben giya na Naira miliyan 500
A wani labarin da Legit Hausa ta kawo maku, hukumar Hisbah ta lalata kayayyakin barasa da suka kai darajar Naira miliyan 500 a kwaryar jihar.
A cikin watan Maris na shekarar 2023 ne lamarin ya faru, inda kwamandan Hisbah Sheikh Sani Harun ya bayyana cewa kotu ce ta basu umurnin lalata kayan.
Jihar Kano na daga cikin jihohin da aka haramta shigowa, sayarwa da kwankwadar barasa, inda aka tanadi hukunci mai tsauri ga wadanda suke karya doka.
Asali: Legit.ng