Bayanai Sun Fito Kan Haduwar Tsohon Shugaban Kasa Buhari da Nasir El-Rufai

Bayanai Sun Fito Kan Haduwar Tsohon Shugaban Kasa Buhari da Nasir El-Rufai

  • Muhammadu Buhari da Nasir El-Rufai sun hadu da juna watanni fiye da shida bayan sun bar ofis a Najeriya
  • Garba Shehu ya sanar da wannan ganawa a yammacin Litinin a dandalin X wanda ya fi shahara da Twitter
  • Mai magana da yawun tsohon shugaban Najeriyan ya ce shi da Nasir El-Rufai sun taba zama abokan karatu

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Daura, Katsina - Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Nasir El-Rufai a gidansa da yake garin Daura da ke jihar Katsina.

Babu mamaki ne wannan ne karon farko da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari zai hadu da Malam Nasir El-Rufai.

Nasir El-Rufai
Nasir El-Rufai a gidan Muhammadu Buhari Hoto: Garba Shehu
Asali: Twitter

Buhari ya zauna da Nasir El-Rufai

Wanda ya sanar da labarin wannan haduwa da shi ne Garba Shehu a matsayinsa na mai magana da yawun shugaba Buhari.

Kara karanta wannan

Shari'ar Kano: Lauya mazaunin Kano ya yi hasashen damar Abba Kabir a Kotun Koli

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malam Garba Shehu ya bayyana haka ne a yammacin ranar Litinin a shafinsa na X.

Mai magana da bakin tsohon shugaban kasar ya kara da cewa shi da El-Rufai tsofaffin abokan karatu ne a shekarun baya.

Garba Shehu ya fitar da sanarwa

"Da ranar nan, na samu damar kasancewa da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya karbi bakuncin tsohon abokin makarantana, Nasir El-Rufa'i wanda ya kawo ziyarar gaisuwa zuwa Daura.
Tsohon shugaban kasar ya yi farin cikin haduwa da tsohon gwamnan."

- Garba Shehu

Legit ta na tunanin tsohon gwamnan na jihar Kaduna da Garba Shehu sun yi karatu a makarantar Barewa College a Zariya.

Malam Nasir El-Rufai ya yi karatun digirinsa ne a jami’ar Ahmadu Bello a Zariya, shi kuma Garba Shehu ya koma Bayero a Kano.

An addabi Buhari a garin Daura

Kara karanta wannan

El-Rufai da tsohon sarkin Kano sun ziyarci Tudun Biri kan bama-bamai da aka jefa wa Musulmai

Kafin zuwan Nasir El-Rufa'i da ‘yan tawagarsa, ‘yan siyasa da-dama sun maida Daura wata Makkarsu tun daga watan Yuni.

Ganin yadda ake zuwa wajensa duk ranar Allah ne Muhammadu Buhari ya yi burin ya tsere zuwa kasar Jamhuriyyar Nijar.

An kai hare-hare a jihar Zamfara

A gefe guda an ji labari har yanzu na kai hare-hare a jihar Zamfara, har an kashe rayuka, wasu kuma suna asibiti da hannun ‘yan bindiga.

Bayanan da aka samu sun ce ‘yan bindiga sun yi shiri mai kyau sun rika zaben gidajen da za su kai hari a cikin karamar hukumar Zurmi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng