Arzikin Tinubu Ya Kai $4Bn? An Gano Makudan Kudaden Da Buhari a Yar’Adua Suka Mallaka

Arzikin Tinubu Ya Kai $4Bn? An Gano Makudan Kudaden Da Buhari a Yar’Adua Suka Mallaka

  • Har yanzu ba a san adadin dukiyar da shugaban Najeriya na 16 kuma na yanzu, Bola Ahmed Tinubu ya mallaka ba
  • Legit ta ruwaito cewa tun da aka kafa dimokuradiyya a 1999, Yar'Adua da Buhari ne kawai suka sanar da dukiyar da suka mallaka
  • A cewar dokar aikin gwamnati da ke a kundin mulkin Najeriya na 1999 (kamar yadda aka sabunta) an bukaci ma'aikata su fadi dukiyar da suka mallaka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja - Masu ruwa da tsaki daga kungiyoyin ma'aikatan gwamnati (CSO), sun yi nuni da cewa bayyana dukiyar da ya mallaka wani nauyi ne da ya rataya kan Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Kungiyar Arewa ta gano dalilin Tinubu na janye sunan El-Rufai, Kwankwaso a nadin ministoci

Kungiyoyin CSO sun ce har yanzu ba wanda ya san dukiyar da Tinubu ya mallaka kuma hukumar da'ar ma'aikata ta yi gum da bakinta kan hakan.

Tinubu/Buhari/Yar'Adua
Mafi akasarin manyan shugabannin Najeriya dattijai ne, maza kuma masu kudi. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Dennis Olounjunne Olawale, Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Jaridar Legit ta fahimci cewa marigayi Umaru Musa Yar'Adua da Muhammadu Buhari ne kawai suka sanar da dukiyar da suka mallaka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan sun ki bin wannan doka ta sanar da dukiyar da suka mallaka har suka sauka daga mulki.

Nawa ne darajar dukiyar da Yar'Adua da Buhari suka mallaka?

Yar'Adua ya bayyana cewa dukiyarsa ta kai Naira biliyan 856 da miliyan 452 da dubu dari 892, inda ya ke samun akalla Naira miliyan 18.7 duk shekara.

Ya kuma bayyana cewa matarsa, Turai, na da dukiyar da ta kai darajar Naira miliyan 19, da suka hada da gidaje.

A shekarar 2015, tsohon shugaban kasa Buhari ya sanar da cewa ya mallaki dukiyar da ta kai darajar Naira miliyan 30, kuma suna a asusun bankinsa.

Kara karanta wannan

Zargin rashawa: Hukumar LASTMA ta kori ma'aikata biyar, ta fara binciken wasu 14

A kasafta dukiyar ta sa, Buhari ya ce ya na da dalar Amurka dubu 150, gidajen kasa guda 2, dabbobi da filaye.

Hasashe: Dukiyar Tinubu ta kai darajar dalar Amurka biliyan 4

Amma a bangaren Shugaba Tinubu, 'yancin samun bayanai (FoI) bai yi tasiri wajen gano adadin dukiyar da ya mallaka ba.

Jaridar Guardian ta ce wani yunkuri da ta yi na tuntubar tsohon shugaban CCB, Isa Muhammed, kan ko Shugaba Tinubu da wasu sun bayyana kadarorin da suka mallaka ya ci tura.

Jaridar ta ruwaito cewa shugaban mai ci a yanzu, idan da ya bayyana dukiyar da ya mallaka, da ya tabbatar ko ya kori jita-jitar da ake yadawa na cewar dukiyarsa ta kai darajar darar Amurka biliyan hudu.

Kungiyar CNYMI ta gano shirin gurgunta siyasar Arewa

A wani labarin, wata kungiyar matasan Arewa ta yi zargin cewa akwai shirin da ake yi na gurgunta siyasar Arewa gabanin zaben 2027, Legit Hausa ta ruwaito.

Kungiyar mai suna CNYMI, ta zayyana sunayen wasu 'yan siyasa daga Arewa da gwamnatin tarayya ta kunyata da suka hada da Nasir El-Rufai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel