Abin da ya hana ni bayyana kudi na-Jonathan

Abin da ya hana ni bayyana kudi na-Jonathan

– Tsohon shugaba Jonathan ya bayyana abin da ya hana sa bayyana kadarorin sa

– Goodluck Jonathan yace ba wannan ne abin da zai gyara Najeriya ba

– Yake cewa babu wani ain boyewa

Jonathan ya fadi abin da ya hana sa bayyanawa Duniya dukiyar da ya mallaka.

Lokacin yana shugaba an yi da shi yayi hakan yace sam.

Sai dai Jonathan din yace bai yi wani laifi ba.

Abin da ya hana ni bayyana kudi na-Jonathan
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

Tsohon shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan ya fadi dalilin da ya hana sa bayyanawa Duniya dukiyar da ya mallaka lokacin da ya hau mulkin kasar. Jonathan a lokacin yace ba abin da ke gaban sa kenan ba.

Jonathan din ya ce hakan da yayi ba laifi bane don kuwa dokar kasa ba ta tilasta sa ba. Kai tsohon shugaban kasar dai yace ko lokacin da yayi hakan a lokacin Marigayi shugaba Yar’adua ba don yana so ba.

KU KARANTA: Zan fadi yadda Buhari ya bani kashi a zabe-Jonatha

Abin da ya hana ni bayyana kudi na-Jonathan
Jonathan bai fadawa Yan Najeriya adadin Dukiyar sa ba

Goodluck Jonathan yake karawa da cewa ba bayyana kadororin da ya mallaka a Duniya bane zai gyara Najeriya ko da cewa ma dai ba wani abin da yake kokarin boyewa kamar yadda Legit.ng ta samu labari.

KU KARANTA: Wani Gwamna yayi abin kunya

Yanzu haka rashin lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari na kara tabarbarewa Ini Jaridar Sahara Reporters har ta kai da bututu ake zura masa abinci ko ruwa. . Fadar shugaban kasa dai ta musanya wannan labari tun jiya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hanyar tona sililin Barayi a Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng