Bayyana kadarorinsa, bin doka, tattalin arziki da yadda ‘Yar’adua ya zama zakka

Bayyana kadarorinsa, bin doka, tattalin arziki da yadda ‘Yar’adua ya zama zakka

A yau 5 ga watan Mayu, 2020 aka cika shekaru goma da rasuwar tsohon shugaban kasar Najeriya watau Marigayi Alhaji Ummaru Musa ‘Yar’adua wanda ya karbi mulki a 2007.

Jama’a su na ta kwararo yabo ga tsohon shugaban kasar wanda ya mutu a kan mulki bayan ya yi ta fama da rashin lafiya. Mun kawo wasu kadan daga cikin inda marigayin ya fita zakka.

1. Bayyana arzikin da ya mallaka

Ummaru ‘Yar’adua ne shugaban da ya fara fitowa gaban Duniya ya fadi adadin dukiyarsa da tarin kadarori, har ma da dukiyar da iyalinsa su ka mallaka, har yanzu babu wanda ya sake yin haka.

2. Bin dokar kasa da tsarin mulki

Marigayi Ummaru ‘Yar’adua ya kasance shugaban da ya rika yi wa umarnin kotu da kundin tsarin mulki biyayya ko da ya sabawa abin da shi ko jam’iyyarsa ta PDP su ke so a wancan lokaci.

3. Yunkurin gyara zabe a Najeriya

Tun ranar farko, ‘Yar’adua ya fito fili ya soki zaben da ya ba shi nasarar zama shugaban kasa. A dalilin haka ya yi alkawarin daukar matakin gyara sha’anin zabe har ya kafa wani kwamiti.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya yabi Yar'adua bayan shekaru 10 da rasuwarsa

4. Rage albashi

Gwamnatin Ummaru ‘Yar’adua ta na cikin wadanda ta yi abin da ba a saba gani ba a Najeriya a yayin da ta rage farashin man fetur. ‘Yar’adua ya rage kudin litar man fetur daga N75 zuwa N65.

5. Karin albashi

Ko da ya ke tun zamanin Yakubu Gowon ma’aikata su ka fara samun karin albashi, ‘Yar’adua ya fara makamancin wannan kokari a kan ma’aikatan tarayya, kuma ya kara albashin Sojoji a 2008.

6. Gyaran bankuna

Shugaba Ummaru ‘Yar’adua ya yi kokarin babbako da bankunan da su ka kama hanyar rugujewa domin ya ceto tattalin arzikin kasar. A dalilin haka ne ya kama wasu manya da ake ji da su.

7. Kawo karshen rikicin Neja-Delta

Ummaru ‘Yar’adua ya kawo karshen rikicin Neja-Delta cikin ruwan sanyi ta hanyar yi wa tsageru lamuni da sharadin daina tada tsaye a yankin mai arzikin mai, hakan ya taimaki tattalin arziki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel