Dakarun Sojojin Sama Sun Sheke Kasurgumin Dan Ta'addan da Ake Nema Ruwa a Jallo

Dakarun Sojojin Sama Sun Sheke Kasurgumin Dan Ta'addan da Ake Nema Ruwa a Jallo

  • Rundunar sojin sama ta Operation Whirl Punch ta yi nasarar kawar da wani ƙasurgumin ɗan ta'adda Yellow Jambros, da sauran ƴan ta'adda da dama a hare-hare ta sama
  • Rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta bayyana hakan a wata sanarwa da kakakinta Edward Gabkwet, ya fitar a ranar Lahadi, 10 ga watan Disamba
  • Gabkwet ya ce ƴan ta’addan sun gamu da ajalinsu nasu ne a lokacin da suke yunkurin tsallaka kogin Jikudna da ke gundumar Galadima Kogo

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Dakarun rundunar sojin sama na Operation Whirl Punch sun yi nasarar kawar da wani shugaban ƴan ta'adda da ke garkuwa da mutane, Yellow Jambros.

Dakarun sojojin sun kuma halaka ƴan ta'adda a harin da suka kai ta sama a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja, cewar rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Rayukan mutum 16 sun salwanta, wasu mutum 27 sun jikkata a wani mummunan hatsarin mota

Dakarun sojin sama sun sheke Yellow Jambros
Dakarun sojin sama sun halaka Yellow Jambros Hoto: Nigerian Airforce HQ
Asali: Facebook

Rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana hakan a wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a da yaɗa labarai, Edward Gabkwet, ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta wacce hanya aka kashe ƴan ta'addan?

Gabkwet ya ce ƴan ta'addan sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke yunkurin tsallaka kogin Jikudna da ke gundumar Galadima Kogo, inda suka nufi hanyar Wurukuvhi a ƙaramar hukumar Chikun, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Ya ce an bi sahun Yellow Jambros tare da tawagarsa daga Zamfara zuwa Neja suna kan babura 13 a kan iyakar jihar Kaduna da Neja inda suka nufi Kusasu a Shiroro, kafin a kai musu harin.

A Kusasu, wasu ƴan ta’adda guda biyar da ke kan babur sun shiga cikin ayarin Yellow Jambros, inda adadin baburan ya kai 18, inda suka nufi gaɓar kogin Jikudna.

Kara karanta wannan

Nasara: Yan bindiga da yawa sun mutu yayin da sojoji suka daƙile hare-hare biyu a jihar arewa

A kalamansa:

“A bakin kogin, ƴan ta’addan da babura 18 sun shiga wani ƙaton kwale-kwale a ƙoƙarinsu na tsallakawa domin haɗuwa da sauran ƴan ta’adda a tsallaken kogin.
"A wannan lokacin ne aka ba da izinin gudanar da kai harin."

Ƴan ta'adda da dama sun halaka

Harin dai ya yi tasiri yayin da ya kashe Yellow Jambros da takwarorinsa, ya lalata baburansu tare da nutsar da jirgin ruwan.

"Duk da cewa ba a saba ganin yadda ƴan ta’addan na tafiya cikin ayarin babura 18 da rana ba, amma a bayyane yake cewa Yellow Jambros da tawagarsa sun dauka cewa an dakatar da kai hare-hare ta sama biyo bayan abin takaici da ya faru a Tudun Biri a jihar Kaduna." A cewarsa.

Kakakin na rundunar ya ce Yellow Jambros da ƴan tawagarsa sun yi garkuwa da mutane da dama a hanyar Abuja zuwa Kaduna da kuma wasu ƙauyuka a jihohin Kaduna, Neja, Katsina, da Zamfara.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace wasu muhimman takardun ƙarar zaben gwamnan Arewa da ke gaban kotu

Dakarun Sojin Sama Sun Halaka Ƴan Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa jiragen yaƙin rundunar sojin sama sun halaka aƙalla sama da mutum 100 da ake zargin mayaƙan ƙungiyar ISWAP ne a jihar Borno.

Jiragen yaƙin na rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadin Kai a yankin Arewa maso Gabas ne suka kai harin a jihar Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng