Harin Bam Kan Masu Mauludi: CDS Ya Nemi Afuwar Yan Najeriya, Ya Yi Muhimmin Alkawari 1
- Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya ya yi magana kan harin bam bisa kuskure da sojoji suka kai a ƙauyen Tudun Biri
- Janar Christopher Musa ya bayyana cewa harin kuskure ne ba da gangan ba domin sojoji ba za su taɓa cutar da farar hula ba
- CDS ɗin ya yi alƙawarin cewa za su tababtar da cewa hakan bai sake aukuwa ba a nan gaba wajen gudanar da ayyukansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Plateau - Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya roƙi ƴan Najeriya da su guji yanke hukunci kan sojoji a harin da jirgi mara matuƙi ya kai ƙauyen Tudun Biri da ke jihar Kaduna.
Ya ce bai kamata a yi wani abu da zai ɓata sunan sojojin waɗanda ke da alhakin magance matsalar rashin tsaro a ƙasar nan ba, cewar rahoton The Nation.
Atiku da Ɗangote sun lale Naira biliyan uku sun baiwa ɗan takarar gwamna a arewa? Gaskiya ta yi halinta
Musa ya yi wannan jawabi ne a wajen bikin yaye SEC 45 na Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabaru ta Ƙasa (NIPSS) da ke Kuru, kusa da Jos.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
CDS ya nemi afuwar ƴan Najeriya
A kalamansa:
"Lamarin ba da gangan ba ne. Muna da nufin kare ƴan Najeriya ne kuma ba za a iya ganin muna kashe su ba."
“Saboda haka, ina so in yi kira ga ƴan Najeriya da kada su yi amfani da wannan lamarin wajen karya wa sojojinmu gwiwa, domin mun ƙuduri aniyar kawo ƙarshen duk wata matsalar rashin tsaro da ke addabar al’ummarmu a halin yanzu."
"Abin da ya faru a Kaduna, abin takaici ne, kuma abin nadama ne. Kuskure ne ba da gangan ba."
Sojoji za su cigaba da kare rayukan al'umma
Babban hafsan tsaron ya bayyana kudurin sojojin na kare mutuncin rayukan bil’adama, ya ƙara da cewa sojoji ba za su taba kai hari ga ƴan kasa masu bin doka ba.
Daga nan sai ya yi kira ga ƴan Najeriya da su yi addu’a tare da tallafa wa sojoji da sauran jami’an tsaro a yunƙurinsu na kawar da duk wani kalubalen tsaro da ƙasar nan ke fuskanta.
Sanatocin Arewa Sun Dira Tudun Biri
A wani labarin kuma, kun ji cewa gamayyar Sanatoci a Arewacin Najeriya sun kai ziyara jihar Kaduna domin jajantawa waɗanda harin bam ya yi ajalinsu.
Tawagar wacce take a ƙarƙashin jagorancin Sanata Abdul Ningi da Sanata Abdul'aziz Yari sun miƙa jajensu ga iyalan mutanen da suka rasa rayukansu.
Asali: Legit.ng