Gwamna Abba Ya Bayyana Wata Muhimmiyar Nasara da Ya Samu a Gwamnatinsa
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi magana kan nasarar da ya samu wajen yaƙi da cin hanci da rashawa a Kano
- Gwamnan ya bayyana cewa ya ceto biliyoyin naira na al'ummar jihar daga zurarewa ta hanyar da ba ta dace ba
- Ya dai bayyana hakan ne a wajen bikin ranar yaƙi cin hanci da rashawa ta duniya wanda hukumar PCACC ta shirya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa ya zuwa yanzu ta ceto biliyoyin naira na jihar ta hanyar toshe hanyoyin da suke zurarewa.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da jawabi a bikin ranar yaƙi da cin hanci da rashawa ta duniya wanda hukumar ƙorafe-ƙorafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC) ta shirya.
Ya bayyana cewa zurarewar kuɗaɗen ya sanya masu riƙe da muƙamai na almubazzaranci da dukiyar jama'a, yayin da aka bar hukumomi, ma'aikatun gwamnati da al'umma cikin wani yanayi na koma baya, cewar rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wacce nasara Gwamna Abba ya samu?
Ya yi bayanin cewa daga cikin manyan nasarorin da gwamnatin ta samu ɗomim tabbatar da ingantacciyyar rasuwa ga al'ummar jihar sun bayyana a fili kan yadda ba ta yarda ko kaɗan da cin hanci da rashawa.
Ya ƙara da cewa kadarorin gwamnati da wasu tsiraru suka samu ba bisa ƙa'ida ba a gwamnatin da ta gabata an ƙwato su inda aka mayar da su domin amfanin al'umma.
Ya cigaba da cewa, gwamnatin ta kuma bayar da fifiko wajen samar da sassan yaƙi da cin hanci da rashawa a cikin hukumomin gwamnati tare da tabbatar da biyan kuɗin fansho da giratuti na ƴan fansho da gwamnatin da ta shuɗe ta yi watsi da su da suka kai Naira biliyan 6.
Gwamna Abba Ya Yi Naɗin Muƙamai
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi wasu sababbin naɗe-naɗen muƙami tare da yi wa wasu karin girma.
Daga cikin waɗanda suka samu ƙarin girma akwai Sanusi Dawakin Tofa wanda ya tashidaga Sakataren yada labarai zuwa Darekta Janar na harkar yada labarai da hulda da jama’a.
Asali: Legit.ng