Tudun Biri: Mutane 416 Sun Mutu Yayin Harin Kuskure Na Sojoji a Kauyuka 16 Cikin Shekaru 9
Jihar Kaduna - A ranar 3 ga watan Disamba ce rundunar sojin Najeriya ta kai harin bam a kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Rundunar daga bisani ta yi martani inda ta ce kuskure ne ya saka su harba bam din a kokarin ya ki da ta'addanci.
Adadin mutanen da su ka mutu
Harin ya yi ajalin mutane fiye da 100 wanda ya jawo Legit ta tattaro irin makamancin haka da ya faru a kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daily Trust ta tattaro cewa mutane 416 sun mutu inda ya shafi kauyuka 16 a cikin shekaru 9.
1. Mutane 10 sun mutu a kauyen Kayamla
A ranar 16 ga watan Maris ta 2014, mutane 10 sun mutu sakamakon kuskuren harin sojin Najeriya.
Lamarin ya faru ne a kauyen Kayamla da ke jihar Borno.
2. Mutane 53 sun mutu a sansanin Rann
A ranar 17 ga watan Janairun 2017, mutane 53 sun rasa rayukansu a harin kuskure na soji a jihar Borno, inda wasu su ka ce mutanen sun kai 115.
3. Mutane 20 sun mutu a kauyen Dalgun
Har ila yau, harin soji ya hallaka mutane 20 a kokarin kai wa 'yan ta'adda hari a kauyen Dalgun duk a jihar Borno a ranar 28 ga watan Faburairun 2018.
4. Harin bam ya hallaka 11 a kauyen Ajia
A Karamar hukumar Birnin Magaji mutane 11 sun mutu sakamakon harin bam daga sojin Najeriya a ranar 11 ga watan Afrilun 2019 a jihar Zamfara.
5. Harin Gajigana da Mainok
Rundunar sojin sama ta kai harin ne a kauyukan Gajigana da Mainok wanda mutane 13 su ka mutu da sojojin kasa 30.
Harin ta faru ne a ranakun 2 ga watan Yulin 2019 da kuma 25 ga watan Afrilun 2021.
6. Harin Buwari da Kwatar Daban Mascara
A ranar 16 ga watan Satumba, harin sojin sama ya yi ajalin manoma 9 a kauyen Buwari da ke jihar Yobe.
Haka nan, masunta 20 sun mutu a kauyen Kwatar Daban Mascara a jihar Borno a ranar 26 ga watan Satumbar 2021.
7. Harin Kuragba da Kunkunni
A ranar 20 ga watan Afrilun 2022, yara shida sun mutu a karamar hukumar Shiroro da ke jihar Niger.
Haka nan, a ranar 6 ga watan Yulin 2022, mutane biyu sun mutu a karamar hukumar Safana sa ke jihar Katsina.
8. Mutane 60 sun mutu a Dansadau
A ranar 17 ga watan Disambar 2022 mutane 60 sun mutu a kauyen Mutunji a yankin Dansadau da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.
8. Mutum 1 ya mutu a kauyen Kwaki
A watan Agustan wannan shekara, mutum 1 ya mutu a harin sojin sama daga sojoji a kauyen Kwaki da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Niger.
Sanatocin Arewa sun dira a Kaduna
Kun ji cewa, Sanatocin Arewacin Najeriya sun dira a jihar Kaduna a yau Asabar 9 ga watan Disamba.
'Yan Majalisun sun kai ziyarar jaje ce ga daukacin mutanen da su ka rasa ransu a harin bam kan masu Maulidi.
Asali: Legit.ng