“Mun Fada Mugun Hannu”: Sheikh Yabo Ya Caccaki Gwamnatin Tinubu Kan Kisan Masu Maulidi a Kaduna
- Babban malamin addininin Musulunci, Sheikh Bello Yabo ya ce 'yan Najeriya sun fada mugun hannu, wanda kuma ya kalubalanci shugabannin Arewa
- Sheikh Yabo ya ce kisan masu maulidi a Kaduna ya tabbatar da cewa akwai matsala a sojin Najeriya, inda ya ce ba wannan ne karon farko na irin harin ba
- Ya ce sojoji na ta zubar da jinin bayin Allah a Arewa da sunan harin kuskure, amma ba a taba yin kuskuren hari a kasashen Yarabawa da Inyamurai ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Sokoto - Shahararren mallamin addinin Musulunci a jihar Sokoto ya ce jinin 'yan Arewa na ta kwarara biyo bayan halin bam kan masu maulidi a Tudun Biri, jihar Kaduna.
A cewar sa, dukkan wasu hare-haren bama-bamai kan fararen hula na faruwa ne a Arewa, babu daya da sojoji su ka taba kai wa yankin Kudu.
Ganganci ne harin sojojin kan fararen hula a Arewa - Sheikh Yabo
A cikin wani faifan bidiyo, da shafin karatuttukan malaman Musulunci ya wallafa a facebook, an ga Sheikh Bello Yabo yana martani kan harin bam da sojoji suka saki kan masu maulidi da ya kashe sama da mutum 100 a Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sa:
"Ba wannan ne karon farko sakin bam kan mutanen da basu ji ba basu gani ba da sunan kuskure sojoji suka yi. Sun yi irin hakan a sansanin 'yan gudun hijira na Borno.
"Haka suka saki bam ya kashe bayin Allah a jihar Yobe, da Nasarawa, yanzu kuma ga shi sun saki wani a Kaduna, ni ba na kallon hakan a matsayin kuskure, lallai akwai matsala"
Ya kara da cewa:
"Har yau, sojoji ba su taba yin kuskuren sakin bam a garuruwan Inyamurai da Yarabawa ba. Kullum dai kan Arewa kuskuren ke fadawa, saboda rashin hadin kan 'yan Arewa.
"Ana zubar da jinanan 'yan Arewa, 'yan bindiga na kashe mu, yunwa na kashe mu, yanzu kuma sojojin da za su kare mu su ma suna kashe mu, lallai akwai matsala, dole mu koma ga Allah."
Sheikh Yabo ya magantu kan tsare Mamu
Sheikh Yabo ya kuma yi ikirarin cewa ana kashe 'yan Arewa ne saboda shugabanninta ba su damu da al'umma ba, kansu kawai suka sani, rahoton Daily Trust.
Malamin ya ce an kama Tukur Mamu kan shiga tsakanin 'yan bindiga da iyalan wadanda aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasa na Kaduna zuwa Abuja, amma har yanzu ba a sako shi ba.
Sheikh Yabo ya ce harin da Sunday Igboho ke kai wa 'yan Fulani a Kudancin kasar ya fi muni kan na Mamu, amma an saki Igboho da ke tsaren a jamhuriyyar Benin.
Kalli bidiyon a kasa:
Harim bam a Kaduna: Amurka ta ba Najeriya shawara
A wani labarin, kasar Amurka ta shawarci Najeriya kan horas da dakarun sojinta wajen amfani da fasahar Artificial Intelligence (AI) yayin kai hare-hare.
Amurka ta kuma jajanta wa al'ummar garin Tudun Biri da ke jihar Kaduna, inda a karshen makon da ya gabata sojoji suka farmake su bisa kuskure, Legit Hausa ta ruwaito.
Asali: Legit.ng