El-Rufai da Tsohon Sarkin Kano Sun Ziyarci Tudun Biri Kan Bama-Bamai da Aka Jefa wa Musulmai
- Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi ziyarci Kaduna kan harin bama-baman soji a taron masu Maulidi
- Manyan jiga-jigan arewan biyu sun ziyarci Tudun Biri domin ta'aziyya da jaje ga al'ummar yankin kan ibtila'in da ya afka masu
- A ranar Lahadi da ya gabata ne sojoji suka yi kuskuren sakarwa yan farar hula da ke bikin Maulidi bama-bamai a yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai da amininsa tsohon Sarkin Kano, Mai daraja Muhammadu Sanusi II, sun ziyarci kauyen Tudun biri da ke jihar Kaduna.
El-Rufai da Sanusi sun isa yankin ne domin jajantawa dangin Musulman da aka kashe a harin bama-baman da sojoji suka yi kuskuren jefawa yan farar hula.

Kara karanta wannan
Tudun Biri: Sanatoci 58 a Arewacin Najeriya sun dira a Kaduna, sun ba da gudunmawa mai tsoka

Asali: Twitter
Khalifan Tijjaniya da tsohon gwamnan na Kaduna sun kai ziyarar ne domin mika ta'aziyya ga yan uwan wadanda suka rasu tare da jajantawa wadanda suka jikkata sakamakon harin sojoji a kauyen Tudun Biri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadimin El-Rufai, Muyiwa Adekeye ne ya sanar da hakan a shafinsa na dandalin X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) @MuyiwaAdekeye.
Shugabannin Tijjaniyya sun ziyarci Tudun Biri
A ranar Lahadi da ya gabata ne kauyen Tudun Biri ya gamu da ibtila'i na sakarwa Musulmai bama-bamai bisa kuskure suna tsaka da bikin Maulidi wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka masu yawan gaske.
Jiga-jigan biyu sun shiga sahun sauran shugabannin kungiyar Tijjaniyya wajen kai ziyarar ne a ranar Juma'a, 8 ga watan Disamba.
Idan za ku tuna, Sanusi shine Khalifan darikar Tijjaniyya a Najeriya.
Ga hotunan ziyarar a kasa:

Kara karanta wannan
Tsagin Abba da Gawuna Sun Rattaɓa Hannu Kan Muhimmiyar Takarda a Kano Gabanin Hukuncin Kotun Koli
Sanusi ya magantu kan harin masu maulidi
A baya Legit Hausa ta rahoto cewa Muhammadu Sanusi II ya aiko ta sakon ta’aziyya ga mutanen Tudun Biri a sakamakon rashin da su ka yi a karshen makon jiya.
Sarkin Kano na 14 ya fitar da ta’aziyyar ne a shafin Twitter kamar yadda Legit ta fahimta.
Asali: Legit.ng