Kotu Ta Umarci Gwamnan PDP Ya Biya Basukan Tsaffin Ciyamomin APC Biliyan 3.4, Ta Ba da Dalili

Kotu Ta Umarci Gwamnan PDP Ya Biya Basukan Tsaffin Ciyamomin APC Biliyan 3.4, Ta Ba da Dalili

  • Kotun Daukaka Kara ta yi hukunci kan basukan naira biliyan 4.8 ga tsaffin shugabannin kananan hukumomi a jihar Oyo
  • Kotun ta umarci Gwamna Seyi Makinde ya biya basukan naira biliyan 3.4 daga cikin basukan bayan ya sallami su a farkon hawashi mulki
  • Kotun ta ba da umarnin ne don biyan basukan tsaffin kananan hukumomin da aka zabe su karkashin jam’iyyar APC wanda gwamnan ya kora

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Oyo – Kotun Daukaka Kara ta umarci Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya biya biliyan 3.4 na bashin tsaffin shugabannin kananan hukumomi.

Biyan basukan na cikin kudaden tsaffin shugabannin kananan hukumomi wanda su ke bin bilyan 4.8, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Kujerun Ciyamomi 31 sun fara tangal-tangal a ranar da gwamnan PDP ya rantsar da su

Kotu ta umarci Makinde biyan basukan biliyan 3.4 na tsaffin ciyamomin APC
Kotu ta tilasta gwamna biyan basukan tsaffin ciyamomin tsohuwar gwamnati. Hoto: Seyi Makinde.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke?

Kotun ta ba da umarnin ne don biyan basukan tsaffin kananan hukumomin da aka zabe su karkashin jam’iyyar APC wanda gwamnan ya kora a farkon hawanshi mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan hukuncin ya tabbatar da umarnin Babbar Kotun Tarayya da ta yi hukunci a watan Afrilu, cewar Channels TV.

Yayin hukuncin a jiya Juma’a 8 ga watan Disamba, alkalan guda uku sun bayyana korar shugabannin da Makinde ya yi a matsayin saba dokar kasa.

Kotun har ila yau, ta umarci Makinde biyan naira miliyan 50 ga tsaffin shugabannin karkashin jagorancin Bashorun Mojeed Bosun.

Su waye ake tuhuma a karar?

Wadanda ake karar sun hada da Gwamna Makinde da kwamisinan shari’a da kwamishinan kananan hukumomi da kuma kakakin Majalisar jihar da sauransu.

Mai Shari’a, Danlami Senchi ya fito da wata takarda da kwamishinan Shari’a ya bayyana cewa za su biya basukan biliyan 4.8 cikin watanni shida.

Kara karanta wannan

Kungiyar Arewa ta bayyana hukuncin da ya kamata Kotun Koli ta yanke a shari'ar jihar Kano

Senchi ya ce kotun ba za ta amince da kwana-kwana na gwamnatin jihar ba inda ta ce ba ta san da basukan ba duk da tabbacin kwamishinan Shari’a.

Kotu ta ci tarar Yahaya Bello miliyan 500

A wani labarin, Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta ci taran Gwamna Yahaya Bello tarar naira miliyan 500 kan take hakkin dan Adam.

Ana zargin Bello da barazana ga rayuwar dan takarar jam’iyyar SDP, Murtala Ajaka wanda ya nemi kariya daga kotun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.