Na Yi Ne Don Mijina, Jarumar Nollywood Ta Bayyana Dalilin Musuluntarta da Kuma Barin Addinin Kirista
- Mercy Aigbe, Jarumar fina-finan Nollywood ta bayyana yadda soyayya ta kwashe ta shiga addinin Musulunci da kuma yin aure
- Jarumar ta ce fara soyayyarta da mijinta Kazeem Adeoti shi ya gyara mata rayuwa tare da shiga addinin Musulunci da radin kanta
- Mercy ta bayyana haka ne yayin wata hirar mata a gidan talabijin na TVC inda ta ce ta ga ranar soyayya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Legas - Jarumar fina-finan Nollywood, Mercy Aigbe ta bayyana dalilin watsar da addinin Kirista.
Aigbe ta ce ta koma addinin Musulunci ne saboda soyayya wacce ta hada ta mijinta a yanzu, Legit ta tattaro.
Mene dalilinta na barin Kiristanci zuwa Musulunci?
Ta ce tana jin dadin zama a addinin da kuma samun salama duk da kalubalen da ta fuskanta musamman daga matarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jarumar ta bayyana haka yayin ganawa da manema labarai inda ta ce mijin nata Kazem Adeoti da aka fi sani da 'Adekaz' na nuna musu zallar kauna.
Ta ce ta koma addinin Musulunci ne don radin kanta ba tare da wani ya tilasta ta ba inda ta ce ta jure kalubale kan haduwarta da Adekaz.
Ku kalli bidiyon da ta sake:
Wasu kalubale Mercy ta fuskanta?
Ta kara da cewa babu matar da za ta ya jure irin kalubalen da ta fuskanta inda ta ce da ba don soyayya ba babu abin da zai sa ta haka.
Mercy a baya ta cire rai da sake yin soyayya bayan aurenta ya rushe cikin wani irin yanayi.
Ta bayyana cewa daga bisani sai Adekaz ya zo mata inda ta yi tunanin gwada sa'arta a kanshi.
Mercy Aigbe ta bayyana darussan da ta koya a aikin hajji
A wani labarin, Jarumar fina-finan Nollywood, Mercy Aigbe Adeoti ta bayyana irin muhimman darussan da ta koya yayin aikin hajji.
Jarumar ta ce abin da ta koya shi ne a Makka babu bambanci a tsakanin mutane daga kalar fata da jinsi da kudi ko talauci inda ta ce a wurin Allah kowa daya ne.
Har ila yau, Jarumar ta bayyana irin wahalar da ta sha a matsayinta na wacce ba ta saba ba.
Asali: Legit.ng