Ayi Hattara: Babbar Gadar Fita Daga Legas Ta Ruguje, Ta Haddasa Cunkoso
- Wani bangare daga babbar gadar Legas ta 'mainland' ta uku ya ruguje yayin da wata tirela ta yi hatsari dauke da babbar kwantena
- Hatsarin wanda ya faru a daren ranar Alhamis, ya jawo cunkoson ababen hawa har zuwa safiyar ranar Juma'a inda aka rage cunkoson
- Gwamnatin jihar Legas ta ce hukumomi na iya bakin kokarin su don ganin an samar da hanyar da ababen hawa za su bi kafin gyara inda ya lalace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Legas - Rahotannin da muke samu yanzu na nuni da cewa babbar gadar Alapere ta rushe sakamakon wata tirela dauke da kwantena da ta hau kanta.
Hatsarin ya faru ne a daren jiya, wanda ya shafi hannun fita daga jihar Legas da ke babbar gadar 'Mainland' ta uku.
Wakilin Tvcnews wanda ya ziyarci wajen ya shaida cewa mutane sun yi dandazo a kan gadar inda wasu suka kwana a nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun bayyana cewa an samu nasarar bude wata hanya da za ta ba ababen hawa damar wucewa.
Gwamnatin Legas ta magantu kan hatsarin
Da ya ke bayar da karin bayani a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a, hadimin gwamnan jihar Legas ta fuskar watsa labarai, Jubril Gawat ya ce mota ta yi karo da gadar ne yayin da take gudu.
Sai dai ya ba da tabbacin cewa za a bude gadar nan ba da jimawa ba sakamakon aiki tukuru da hukumomi ke yi a wajen da hatsarin ya faru.
Ya wallafa cewa:
"Da misalin karfe 11 na daren jiya, tirela da ke shiga jihar a tsananin gudu ta yi karo da gadar Alapere tare da lalata hannun masu fita daga jihar.
"Tuni hukumar kiyaye hadurra ta jihar Legas @followlastma da kuma mai tallafawa gwamna kan sufuri @sola_giwa da hukumar agajin gaggawa ta jihar suka isa inda hatsarin ya faru, a can suka kwana don ba da agaji."
Ya kara da cewa rundunar 'yan sanda na shiyyar Alapere su ma sun ba da gagarumar gudunmawa tsawon wannan dare.
Duba abin da ya wallafa a kasa:
Edo: Dan dako da baro ya kashe mai karbar haraji kan naira hamsin
Mazauna birnin Edo sun shiga tashin hankali bayan da wani mai dan dako da baro ya kashe wani mai karbar haraji.
Legit Hausa ta ruwaito cewa rigima ta hada su, lokacin da mai karbar harajin ya nemi dan dakon ya biya naira hamsin kudin tikiti.
Asali: Legit.ng