Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Sababbin Nade Naden Mukamai a NPC da Hukumar NCDMB
- Bola Ahmed Tinubu ya ba karamin ministan harkokin man fetur watau Heineken Lokpobiri matsayi a hukumar NCDMB
- Shugaban kasa ya nada Felix Ogbe ya canji Simbi Wabote wanda wa’adinsa ya kare a matsayin shugaban hukumar
- Akwa Effion Okon da Alhaji Mohammed Mustapha Bintube sun samu matsayi a NPC mai cefanar da kayan gwamnati
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada shugabanni da majalisar da za ta rika sa ido a game da aikin hukumar NCDMB.
Mai taimakawa shugaban kasa na musamman wajen yada labarai da hulda da jama’a, Ajuri Ngelale ya fitar da sanarwar nan.
Bola Tinubu ya nada mukamai
A jawabin Ajuri Ngelale na ranar Alhamis, ya ce an yi amfani da sassa na 71 (1), 72 da 73 na dokar mai a wajen nadin mukaman.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganin wa’adin Simbi Wabote na shekaru hudu ya cika, sai aka nada Felix Ogbe ya zama sabon shugaban hukumar NCDMB ta kasa.
A shekarar 2020 Muhammadu Buhari ya amince Wabote ya kara yin shekaru hudu a ofis.
An ba Heineken Lokpobiri mukami
Mista Ngelale ya bada sanarwar cewa karamin Ministan harkar mai, Heineken Lokpobiri zai zama shugaba (HOM) na hukumar.
Jaridar The Cable ta ce sauran wadanda za su kula da NCDMB su ne; mataimakin shugaban kamfanin NNPCL, Oritsemyiwa Eyesan.
Akwai shugaban NUPRC, Gbenga Komolafe da Bekearedebo Warrens wanda aka dauko daga ma’aikatar harkokin mai na tarayya.
Ragowar su ne: shugaban Zitadel Limited, Nicolas Odinuwe da kuma Olorundare Thomas, Rapheal Samuel da Alhaji Sadiq Abubakar.
Gwamnati ta yi karin shugabanni a NPC
Wani rahoto daga The Nation ya ce shugaba Tinubu ya nada karin mutane da za su jagoranci majalisar cafanar da kayan gwamnati.
Sanarwar ta ce Oluwole Osin, Mohammed Mustapha Bintube, Olayiwola Yahaya da Akwa Effion Okon, sun samu kujeru a majalisar NPC.
Ina makomar matatun Najeriya?
Duk da alkawarin da kamfanin NNPCL ya yi, wani rahoto ya nuna ba dole ba ne matatar da ake jira ta soma aiki a Disamban 2023.
Gwamnatin Muhammadu Buhari ta kashe biliyoyi masu yawa domin a iya tace mai a cikin gida, Alex Ogedengbe yana ganin duk a banza.
Asali: Legit.ng