Buhari ya sabunta nadin shugabannin PTDF, PEF da NCDMB

Buhari ya sabunta nadin shugabannin PTDF, PEF da NCDMB

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sabunta nadin shugabannin hukumomin PTDF, PEF da NCDMB

- Sanarwar sabunta nadin ta fito ne daga bakin Mista femi Adesina, kakakin Shugaba Muhammadu Buhari

- Sanarwar ta ce dukkan shugabannin uku sun taka rawa gani a bangarorinsu tare da samun nasarori shi yasa aka sabunta nadinsu

Shugaba Muhammadu Buhari ya sabunta nadin Dakta Bello Aliyu Gusau a matsayin sakataren hukumar asusun cigaban fasahar man fetur (PTDF) da Ahmed Bobboi a matsayin shugaban asusun PEF.

A sanarwar da ya fitar na sabunta nadin a ranar Juma'a a Abuja, Kakakin Buhari, Femi Adesina ya kuma ce an sabunta nadin Simbi Wabote a matsayin sakataren hukumar kula da fasahar cikin gida (NCDMB).

DUBA WANNAN: APC ta dakatar da hadimin Buhari, surukin Tinubu da wasu mutane takwas

Buhari ya sabunta nadin shugabannin PTDF, PEF da NCDMB
Buhari ya sabunta nadin shugabannin PTDF, PEF da NCDMB. Hoto daga @Bashirahmaad
Asali: Twitter

Ya ce an sabunta nadin bayan karamin ministan man fetur, Timpre Sylva ya mika sunayensu ga shugaban kasa.

Adesina ya ce Aliyu ya yi jagoranci mai inganci a PTDF na shekaru hudu da suka shude bisa tsarin bawa wasu bangarori bakwai muhimmanci da aka gabatar a 2017.

KU KARANTA: Borno: Sojoji sun kashe manyan kwamandojin 'yan Boko Haram 7 a Tafkin Chadi

Bangarorin sun kunshi rage kashe kudade, inganta ayyukan cikin gida, sada masana'antu, samar da kudaden aiki, amfani da cibiyoyin ayyuka na gida Najeriya da binciken kimiyya na cikin gida.

A cewarsa, an sabunta nadin Bobboi ne saboda muhimmiyar rawar da ya taka wurin sauye sauye a bangarorin samar da iskar gas da fetur da sauransu.

Ya ce shugaban NCDMB, Wabote shima ya yi aiki tukuru wurin jagoranci mai kyau a hukumar da kuma kammala ginin hedkwatar hukumar.

Hadimin shugaban kasar ya kuma ce Wabote ya kara ayyuka da dama da suka janyo masa yabo a bangaren aikinsa.

Dukkan nade-naden za su fara aiki nan take a cewar sanarwa.

Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya lashe kyautar Zik a rukunin shugabanci na shekarar 2019 kamar yadda Farfesa Pat Utomi ya sanar a ranar Alhamis.

Zulum wanda shine mutum na takwas cikin jerin wadanda suka lashe kyautar an karrama shi ne saboda shugabanci na gari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel