An Kuma: Yan Bindiga Sun Ƙai Sabon Hari, Sun Yi Garkuwa da Ɗaliban Jami'ar Tarayya Ta Arewa
- Yan bindiga sun ƙara yin garkuwa da ɗalibai da yawa na jami'ar tarayya da ke Lafia a jihar Nasarawa
- Mazauna garin Gandu, yankin da jami'ar take sun bayyana cewa maharan sun kai farmaki tare da sace ɗaliban ranar Laraba
- Hukumar jami'ar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce har yanzun ba a san adadin ɗaliban da aka sace ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Nasarawa - Wasu miyagun ‘yan bindiga sun kai sabon farmaki ƙauyen Gandu, sun yi garkuwa da wasu dalibai a jami’ar tarayya da ke Lafia.
Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya bayanansa, ya shaida wa Daily Truat cewa da farko ƴan bindiga sun shiga garin da misalin ƙarfe 7:30 na dare ranar Laraba.
Da zuwa suka buɗe wuta a kan iska da nufin tsoratar da mutane amma da suka fahimci jami'an tsaro sun tunkaro yankin, sai suka gudu suka buya na tsawon awanni a cikin daji.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani ganau da ya nemi a ɓoye sunansa ya bayyana cewa ƴan bindiga sun farmaki wani Otal na taro dake kan titin Makurdi da karfe 2:00 na dare wayewar garin Alhamis.
A cewarsa, maharan sun samu nasarar tafiya ɗaliban jami'ar tarayya ta Lafiya guda biyar a wurin.
Majiyar ta ce ‘yan bindigan sun sake komawa Gandu, garin da ɗalibai ke zama da ke daura da wurin da jami’ar take, suka buɗe wuta bisa tilas ɗalibai suka fito daga gidajensu.
Yayin haka ne maharan suka yi awon gaɓa da ɗalibai biyar yayin da wasu da dama suka samu raunuka, a cewar majiyar.
Ɗalibai guda nawa yan bindigan suka sace?
Mai magana da yawun jami'ar, Abubakar Ibrahim, ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Punch, yana mai cewa har yanzun ba a tantance adadin ɗaliban da aka sace ba.
A kalamansa ya ce:
"Ya yi wuri a iya tantance adadin daliban da suka sace saboda wadanda abin ya shafa ba a cikin harabar makaranta suke zaune ba a gidajen haya na wajen makarantar suke rayuwa."
"Daga bayanan muka samu, adadin daliban da aka sace ya kai tsakanin uku zuwa biyar. Ko yaya ne dai jami'a tana aiki tuƙuru don tabbatar da cewa duk ɗalibai sun koma cikin harabar makaranta."
'Yan Bindiga Sun Ƙara Kai Mummunan Hari Ƙauyuka 4 a Arewa
A wani rahoton na daban Yan bindiga sun kai sabbin hare-hare wasu ƙauyaka a jihar Sakkwato sun kashe mutane akalla 9 ranar Litinin zuwa Talata.
Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun kuma sace wasu da mutane da dama har da mata da kananan yara.
Asali: Legit.ng