Gwamnatin Zamfara Ta Kwato Motoci 50 Daga Hannun Matawalle, Ta Bayyana Dalili
- Bayan an dade ana kai ruwa rana, gwamnatin jihar Zamfara ta ƙwato motoci 50 a hannun tsohon Gwamna Matawalle
- Mai magana da yawun gwamnan jihar, Sani Sambo, shi ne ya tabbatar da hakan ga manenma labarai a ranar Asabar
- Ya bayyana cewa an ƙwato motocin ne a gidajen Matawalle bayan kotu ta yi watsi da ƙarar da ya shigar ta neman a hana ƙwace motocin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta ce ta ƙwato motoci kusan 50 da ake zargin tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle ya yi awon gaba da su.
Sani Sambo, mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, shi ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Alhamis, 7 ga watan Disamban 2023, cewar rahoton Channels tv.
Meyasa aka ƙwato motocin?
Sambo ya ce matakin ya biyo bayan hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke Sokoto ta yanke a ranar Juma'ar da ta gabata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce an bi tsarin da ya dace domin kwato motocin daga gidajen Gusau da Maradun na tsohon gwamnan wanda a baya ya musanta cewa ya mallaki wata kadara ta gwamnati a lokacin da yake barin kujerar gwamna.
Sambo ya bayyana cewa gwamnatin da Gwamna Dauda Lawal ke jagoranta tana yin duk mai yiwuwa don ganin an kawo cigaban da ake so a jihar amma ba wai don farautar kowa ba ko kuma ɓata sunan wani.
Batun motocin ya jawo cece-kuce
Lokacin da Gwamna Lawal ya karɓi mulki a matsayin gwamnan Zamfara a ranar 29 ga Mayu, 2023, an yi ta cece-kuce kan sace motoci a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau.
Daga baya jami'an tsaro sun kai samame gidaje biyu na Matawalle a ƙananan hukumomin Gusau da Maradun inda suka ƙwato wasu motoci.
Cikin gaggawa tsohon gwamnan ya garzaya kotu inda ya samu umarni hana gwamnatin jihar kwace motocin, har zuwa lokacin da kotun ta yanke hukunci kan lamarin.
A cewar gwamnatin jihar, kotun mai zama a Sokoto ta yi watsi da ƙarar da tsohon gwamnan ya shigar.
Matawalle Ya Garzaya Kotu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma miniatan tsaro, Bello Matawalle, ya garzaya kottun ɗaukaka ƙara.
Matawalle ya garzaya kotun ne domin ƙalubalantar hukuncin wata babbar kotu na yin umarni da a ƙwace masa motoci 50.
Asali: Legit.ng