"Ba za ta sabu ba": Sanatan FCT ta farwa Wike kan wasu ayyuka a Abuja, bidiyo ya yadu
- An caccaki ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, kan aiwatar da ayyukan da ba su dace da tsarin rayuwar jama’a ba
- Ireti Kingibe, sanata mai wakiltar birnin tarayya, ta balbale shi da fada yayin wani taron masu ruwa da tsaki da ministan
- Sai dai Wike ya ce ba gwamnatin Shugaba Tinubu bace ta yi watsi da ayyukan, kuma bai kamata gwamnatin da ta karbi mulki ta yi watsi da ayyukan da suka lakume biliyan 40 ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Ireti Kingibe, sanata mai wakiltar babban birnin tarayya, ta caccaki Nyesom Wike, ministan Abuja, ta na mai cewa ayyukansa a babban birnin tarayya ba su dace da tsarin rayuwar al'umma ba.
A wani bidiyo da Legit Hausa ta gani, sanatar ta yi bayanin cewa motocin bas da ministan yake shirin samarwa abu ne da aka taba yin su a baya, kuma basu cimma nasara ba. Ta ce, "cikin yan shekaru, da zaran wa'adinka ya kare, gaba daya motocin bas din za su mutu.
Dalilin da yasa Kingibe ta balbale Wike da fada
Ta ci gaba da yin tsokaci kan motocin bas din CNG da ministan ya bayyana a baya cewa, bisa la’akari da tantance su, kadan ne kawai za su iya gyaruwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kingibe ta ce:
"Mun bincika wadannan motocin bas din, kuma an fada mana cewa yan kadan daga cikinsu ne za a iya gyarawa. Saboda haka, dole za ka bukaci siyan sabbin motocin bas, wanda babu hankali a cikin siyan motocin bas da za su yi aiki da fetur ko diesel a wannan lokaci."
Ta kuma caccaki shirin gina gidan tarihi, tana mai cewa aikin na manyan mutane ne kuma ba zai yi ma'ana ga mutanen birnin tarayya da ke neman taimako ba.
Wike ya mayarwa sanatar Abuja martani
Sai dai kuma a martaninsa, Wike ya ce gwamnatin Shugaban kasa Bola Tinubu ba ita ta bayar da wadannan ayyuka ba, a cewarsa, gwamnatocin baya ne suka bayar da kwangilar kuma bai kamata ace wata gwamnati ta yi watsi da ayyukan da gwamnatocin baya suka watsar ba.
A wajen ministan, aikin na da muhimmanci ga kasar saboda wata gwamnati na iya kashe biliyan 40 sannan gwamnatin da za ta karbi mulki ta yi watsi da wannan aiki.
Kalli bidiyon a kasa:
Gwamnatin Tinubu ta fara raba N20,000
A wani labarin kuma, mun ji cewa gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta mayar da hankali sosai wajen cimma ajandarta na sabonta fata.
Hakan ya kasance ne yayin da Ma'aikatar jin kai da kawar da talauci karkashin jagorancin Dr Betta Edu, ta kaddamar da shirin rabawa marasa karfi N20,000 a jihar Kogi, a ranar Talata, 5 ga watan Disamba, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Asali: Legit.ng