Oshiomole Ya Gaya Wa NLC Abu 1 da Za Ta Yi Wa Ma'aikata Kafin Kirsimeti
- Sanata Adams Oshiomhole ya ce ya kamata a biya ƙarin albashin N35,000 ga ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu
- Oshiomhole ya ce ya kamata NLC ta tabbatar da biyan albashin ma’aikata domin rage tasirin cire tallafin man fetur kafin Kirsimeti
- Tsohon gwamnan jihar Edo ya ce ƙarin albashin yarjejeniya ce kuma dole ne a tabbatar da ita a kowane mataki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya ce ya kamata a biya ma'aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu ƙarin N35,000 don rage tasirin cire tallafin man fetur kafin Kirsimeti.
Oshiomhole ya bukaci ƙungiyoyin kwadago da su tabbatar da biyan albashin ma’aikata a fadin jihohi 36, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Ya bayyana haka ne a taron wakilai karo na takwas na ƙungiyar NASU a Abuja a ranar Talata 5 ga watan Disamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wacce buƙata Oshiomole ya nema?
A kalamansa:
Yanzu da aka ƙara N35,000, akwai ma'aikata daga jihohi daban-daban, shin waɗannan jihohin sun aiwatar da ƙarin? Meyasa ba a biya ba kuma sun kwantar da hankalinsu? Mambobin ku ba su cikin jindaɗin a jihohi. Kamata ya yi a ce kowa an ba shi."
"Dole ƙarin albashin N35,000 ya shafi dukkan ma'aikata. Ya kamata a ce kowane ma'aikaci a Najeriya, ma'aikacin gwamnati ne ko na kamfanoni masu zaman kansu, ya samu ƙarin. Wannan shi ne amfanin yin yajin aiki gama-gari."
"Maganar gaskiya itace, buƙatar dole ne ta shafi kowane ma'aikaci a ɓangaren gwamnati ko kamfanoni masu zaman kansu. Da zarar an ce an cimma yarjejeniya, dole ne a yi mata biyayya a kowane mataki."
Oshiomole ya shawarci NLC
Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, ya ƙara da cewa ƙarin albashin na N35,000 bai kamata a ce wasu kawai aka yi wa ba, dole ne NLC ta tabbatar ƙarin ya shafi kowane ɓangare a ƙasar nan.
"Ku gaya wa shugaban NLC cewa waɗannan su ne batutuwan da za su warware, ta yadda a wannan Disamban ka da wanda ya ƙi samun ƙarin N35,000." A cewarsa.
"Ko da kuwa wannan ma'aikacin yana aiki ne a matakin tarayya, jiha, ƙaramar hukuma ko kamfanoni masu zaman kansu, dole ne a biya wannan N35,000. Idan ba ka biya ba babu kai babu Kirsimeti a matsayinka na mai ɗaukar aiki."
An Fara Biyan Albashin Ma'aikatan da Aka Rike
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta fara biyan albashin ma'aikata da aka riƙe.
Ma'aikatan dai an biya su albashin na watan Nuwamba ne bayan an riƙe shi saboda matsalar da suka samu da IPPIS.
Asali: Legit.ng