An Shiga Jimami Yayin da Aka Kashe Dalibin Jami'a Domin Yin Tsafi, Bidiyo Ya Bayyana

An Shiga Jimami Yayin da Aka Kashe Dalibin Jami'a Domin Yin Tsafi, Bidiyo Ya Bayyana

  • Jami’an rundunar ƴan sandan jihar Ogun sun kama waɗanda ake zargin sun kashe wani ɗalibin jami’ar OAU ɗan 100L, Quadri Salami
  • Kamar yadda wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan, Omolola Odutola ta fitar, wasu mutum biyu sun daddatsa muhimman sassan jikin Salami domin gudanar da tsafi
  • Waɗanda ake zargin su biyu sun siyar da sassan jikin ɗalibin ga masu damfara ta intanet (Yahoo Yahoo)

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Abeokuta, jihar Ogun - Rundunar ƴan sandan jihar Ogun ta ce ta gano dalilin ɓacewar wani ɗalibi mai suna Quadri Salami, wanda ya ke a 100L a jami’ar Obafemi Awolowo (OAU).

A ranar 14 ga Nuwamba, 2023 mahaifin Salami ya kai rahoto a ofishin ƴan sanda na Kemta a jihar Ogun cewa ɗansa ya ɓace, inda ya ce tun ranar 8 ga watan Nuwamba bai sanya ido kan ɗansa ba, kuma duk ƙoƙarin gano shi ya ci tura.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya halaka ya halaka matarsa a Burtaniya kan abu 1 rak

Miyagu sun halaka dalibin jami'ar OAU
Sun dai siyar da sassan jikinsa ga yan Yahoo-Yahoo Hoto: @OgunPoliceNG
Asali: Twitter

Ƴan sanda sun tono gawar ɗalibin OAU da ta ruɓe

A wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan jihar Omolola Odutola ta fitar a daren Laraba, 6 ga watan Disamba, rundunar ƴan sandan ta ce kwamishinan ƴan sandan, Alamutu Abiodun Mustapha ya samu gagarumar nasara kan binciken.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Omolola ta ce an samu nasarar ne a lokacin da ya jagoranci tawagar ƴan sanda zuwa Mile 6 a unguwar Ajemo da ke Abeokuta, zuwa wani kabari mara zurfi domin tono sassan jikin mamacin da suka ruɓe bayan wata na'urar bibiya da aka sanya wa wani mai suna Akeem Usman.

An kama Akeem yana riƙe da wayar marigayin ɗan shekara 18.

Ya suka yi da gawar marigayin?

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

Ya faɗi sunan wani Ifadowo Niyi wanda ya ce tare suka aikata wannan mummunan aiki ta hanyar yanka Quadri da daddatsa muhimman sassan jikinsa domin yin tsafi."

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da aka dasa bam a babbar jami'ar Najeriya, yan sanda sun yi bayani

"Ifadowo ya tafi da kan Quadri da hannayensa biyu, sannan ya tura naira dubu 100 a asusun Akeem Usman a matsayin kasonsa na sassan jikin da aka siyar."
"Daga nan wanda ake zargin ya cigaba da siyar da sassan jikin marigayin ga masu buƙata ƴan damfarar yanar gizo, sannan ya binne zuciya, kafafuwa biyu da tsoka a cikin wata roba domin yin tsafi, sannan ya yi amfani da sauran gangar jikin domin Awure."
"Daga cikin bayanan da suka bayar, waɗanda ake zargin sun bayyana yin amfani da kawunan wasu mutum huɗu domin yin tsafin samun kuɗi wanda aka fi sani da "Osole"."

Yanzu haka waɗanda ake zargin suna hedikwatar ƴan sanda da ke Eleweran a sashen SCID domin cigaba da bincike. Ƴan sanda sun yi alƙawarin cewa za a gurfanar da su a gaban kuliya.

Ƴan Sanda Sun Cafke Ƴan Yahoo-Yahoo

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Rivers ta samu nasarar cafke wasu ƴan damfarar intanet watau Yahoo-Yahoo.

Ƴan sandan sun cafke waɗanda ake zargin bisa aikata laifin birne wani jariri donin neman duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel