Yayin da Ake Dakon Hukuncin Kotun Koli, Hukumar NJC Ta Yi Abu 1 Don Inganta Bangaren Shari'a

Yayin da Ake Dakon Hukuncin Kotun Koli, Hukumar NJC Ta Yi Abu 1 Don Inganta Bangaren Shari'a

  • Hukumar Shari'a a Najeriya, NJC ta amince da karin girma ga wasu alkalai zuwa Kotun Koli a yau Laraba
  • Sabbin alkalan guda 11 sun samu karin girman ne zuwa Kotun Koli bayan sahalewar hukumar ta Shari'a
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na hukumar, Soji Oye ya fitar a yau Laraba 6 ga watan Disamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Hukumar Shari'a a Najeriya (NJC) ta kara wa alkalai 11 karin girma zuwa Kotun Koli.

Wannan na zuwa ne yayin da ake dakon hukuncin Kotun Kolin a jihohi da dama kan shari'ar zabe, cewar Premium Times.

Hukumar NJC ta amince da karin girma ga alkalai 11 zuwa Kotun Koli
Alkalai 11 sun samu karin girma zuwa Kotun Koli. Hoto: Olukayode Ariwoola.
Asali: UGC

Yaushe alkalan su ka samu karin girma?

Kara karanta wannan

Haka siddan sojoji suka fara sakar mana bama-bamai, inji wadanda suka tsira cikin masu Maulidi

Sanarwar karin girman na kunshe ne a cikin bayanin da daraktan yada labarai na hukumar, Soji Oye ya fitar a yau Laraba 6 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabbin alkalan da su ka samu karin girman za a rantsar da su ne bayan kammala tantance su da Majalisa za ta yi.

Daga bisani za su kama aiki bayan Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da su a fadarsa, cewar Channels TV.

Su waye su ka samu karin girman?

Da wannan nadin na sabbin alkalai, Kotun Koli yanzu ta na da alkalai 21 kamar yadda kundin tsarin mulki ta tanadar.

Daga cikin jerin wadanda su ka samu karin girman akwai:

1. Mai Shari'a, Jummai Hannatu Sankey

2. Mai Shari'a, Chidiebere Nwaoma Uwa

3. Mai Shari'a, Chioma Egondu Nwosu-Iheme

4. Mai Shari'a, Haruna Simon Tsammani

Kara karanta wannan

Maulidi: Atiku ya yi martani kan harin bam da aka yi kan bayin Allah a Kaduna, ya ba da shawara

5. Mai Shari'a, Moore Aseimo A. Adumein

6. Mai Shari'a, Obande Festus Ogbuinya

7. Mai Shari'a Stephen Jonah Adah

8. Mai Shari'a, Habeeb Adewale O. Abiru

9. Mai Shari'a, Jamilu Yammama Tukur

10. Mai Shari'a, Abubakar Sadiq Umar

11. Mai Shari'a, Mohammed Baba Idris

Ariwoola ya rantsar da sabbin alkalai

Kun ji cewa, Alkalin alkalan Najeriya, Olukayode Ariwoola ya rantsar da sabbin alkalan Kotun Daukaka Kara guda tara.

Wannan na zuwa ne bayan karin girma da alkalan su ka samu su mutum tara a kwanakin nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.