Mutane Sun Yi Zanga Zanga a Majalisa, Sun Nemi Minista Ya Sauka Bayan Tono Laifuffukansa

Mutane Sun Yi Zanga Zanga a Majalisa, Sun Nemi Minista Ya Sauka Bayan Tono Laifuffukansa

  • Nyesom Wike ya gamu da fushin wasu kungiyoyi, mazauna da 'yan asalin garin Abuja a ofis
  • Daruruwan jama’a su ka shirya zanga-zanga har gaban majalisa domin ayi waje da Ministan
  • Wasu cikin tsare-tsaren da Nyesom Wike ya fito da shi sun jawo masa matsala da al’umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Dubban mazauna garin Abuja su ka shirya zanga-zanga domin ganin Nyesom Wike ya sauka daga kujerar da yake kai a yau.

Sahara Reporters ta ce masu zanga-zangar sun yi kira ne ga Nyesom Wike ya yi murabus daga matsayinsa na Ministan birnin Abuja.

Zanga-zangar ta hada da kungiyoyi masu zaman kan su da wasu da ke zama a Abuja wadanda ba su ji dadin ayyukan babban Ministan.

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisan da aka Yi tun 1992 sun tuno tsohon bashin da su ke bin Gwamnati

Wike.
Zanga-zanga a kan Nyesom Wike a Abuja Hoto: saharareporters.com
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike: Kungiya ta jagoranci zanga-zanga

Adamu Kabir Matazu wanda yana cikin wadanda su ka shirya zanga-zangar a majalisar tarayya ya bukaci a binciki Nyesom Wike.

Shugaban kungiyar ta Network of Civil Societies for Economic Sustainability ya zargi Ministan da badakalar filaye a birnin tarayyar kasar.

Meyasa ake so Nyesom Wike ya tafi?

"Mun hada-kai domin nuna damuwarmu a kan umarnin da aka bada a birnin tarayya a karkashin jagorancin Nyesom Wike.
Abin takaici ne birnin Abuja ya zama tushen hayaniya saboda danyen ayyukan Wike, wanda ke kokarin kawowa manufar Tinubu matsala tare da taba nagartar gwamnatin tarayya.
Mun zo nan yau ne domin mu bukaci murabus din Wike da gaggawa tare da bincike da gurfanar da shi a matsayin Ministan Abuja."

- Adamu Kabir Matazu

Rahoton ya ce Matazu ya zargi tsohon gwamnan na Ribas da rashin sanin aiki da kuma gaza tabuka abin da ake bukata a gwamnati.

Kara karanta wannan

Jama’a Sun Jero Bukatunsu Wajen Zanga Zanga a Kaduna a Dalilin Kashe 'Yan Maulidi

Zargin da ke wuyan Wike a Abuja

Kamar yadda aka gani a bidiyo, masu zanga-zangar sun nemi Bola Tinubu ya tsige Ministan idan har ba zai ajiye aikin da kan shi ba.

Masu zanga-zangar sun lissafo mugayen tsare-tsare, karbe filayen jama’a da yakar mutanen wani yanki na kasar a cikin laifuffukansa.

Wike da rikicin cikin jam'iyyar PDP

Ana da masaniya cewa an fara lissafin wanda zai zama sabon shugaban jam'iyyar adawa ta PDP bayan an yi waje da Dr. Iyorchia Ayu.

Sunayen wasu tsofaffin Gwamnoni sun fara yawo, ana zargin Nyesom Wike wanda yake aiki da APC yana da ’yan takaransa a jam’iyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng