Ana Jimamin Harin Sojoji Kan Masu Maulidi, Dakarun Sojoji Sun Sheke Masu Ba Yan Bindiga Bayanai
- An rage mugun iri na masu ɗaukar bayanai suna ba ƴan bindigan da suka addabi bayin Allah a jihar Kaduna
- Dakarun sojoji ne suka yi nasarar halaka masu ba ƴan bindigan bayanai a ƙauyen Kohoto da ke ƙaramar hukumar Kagarko
- Sojojin sun kuma cafke wasu mutum shida masu ba ƴan bindigan bayanai bayan an yi caraf da shugabansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Sojoji sun harbe wasu da ake zargin masu ba ƴan bindiga bayanai ne mutum uku a jihar Kaduna.
Sojojin sun halaka miyagun ne tare da cafke wasu mutum shida a ƙauyen Kohoto da ke kusa da Janjala a ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Ta wacce hanya aka halaka miyagun?
Wani mazaunin Janjala, Abdullahi Zayyanu, ya ce kisan tare da kame waɗanda ake zargin ya biyo bayan kama shugabansu, Mu’azu, wanda ake kira da Baushe a Kagarko a makon jiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa:
“Mu’azu, wanda ake kira da Baushe, ya je kasuwar Kagarko a makon da ya gabata ya saya wa mutanensa kayan abinci da tabar wiwi, nan da nan aka sanar da sojoji, suka je suka cafke shi.”
Ƴan bindiga dai sun addabi al'ummar yankin Akoti, Gundiri, Taka-Lafiya, Sadauna, Dutse da Janjala a ƙaramar hukumar Kagarko.
Sai dai babu wani martani daga kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna kan wannan lamarin.
Dakarun sojoji sun cafke masu ba ƴan bindiga bayanai
Dakarun sojoji sun kama wasu mutum uku da ake zargin masu ba ƴan bindiga bayanai ne a wani shingen bincike mai nisa kaɗan da garin Kagarko, hedikwatar ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.
Wani mazaunin yankin ya tabbatar da cewa waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu yayin da ake yi musu dukan tsiya da cewa wasu ƴan bindiga ne suka aike su domin su siyo musu tabar wiwi, ƙwayoyi da giya.
Ƴan Sanda Sun Sheke Ƴan Bindiga 50
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan sanda tare da haɗin gwiwar ƴan sakai da sojoji sun samu nasarar halaka ƴan bindiga 50 a yayin wani artabu a jihar Taraba.
Jami'an tsaron sun samu wannan gagarumar nasarar ne a wata fafatawa da suka yi da ƴan bindigan a ƙaramar hukumar Bali ta jihar.
Asali: Legit.ng