Ba Yau Aka Fara Ba: Kwankwaso Ya Yi Tir da Sojojin da Su ka Kashe Mutane a Kaduna

Ba Yau Aka Fara Ba: Kwankwaso Ya Yi Tir da Sojojin da Su ka Kashe Mutane a Kaduna

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya shiga sahun wadanda su ka jajantawa mutanen Tudun Biri a kan abin da ya faru da su
  • ‘Dan siyasan ya koka kan abin da ya faru, yake cewa ba yau sojoji su ka soma hallaka mutanen da ba su yi laifi ba
  • Kwankwaso ya bada shawara cewa gwamnatin tarayya ta yi bincike sosai game da abin da sojoji su ka kira kuskure

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Rabiu Musa Kwankwaso ya yi maza ya fitar da jawabi a sakamakon kashe wasu mutane da aka yi a Tudun Biri a Kaduna.

A yammacin ranar Talata, 11 ga watan Disamba 2023, Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya fitar da jawabi a shafin X da aka fi sani Twitter.

Kara karanta wannan

Sukar Gwamnatin Tinubu Ta Jawo Kashim Shettima Ya Yi wa Peter Obi Tsirara a Siyasa

Kwankwaso
Rabiu Musa Kwankwaso ya soki kisan mutane a Kaduna Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Abin da ya faru a Kaduna akwai takaici -Kwankwaso

‘Dan takaran shugaban kasar na jam’iyyar NNPP a zaben 2023 ya nuna takaicinsa game da yadda aka rasa wadannan mutane a Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rabiu Kwankwaso ya ce wannan mummunan lamari da aka kira da ‘kuskure’ ya sake nuna irin danyen aikin jami’an tsaron kasar.

Kwankwaso ya ce ayi bincike, a biya diyya

A jawabin da ya fitar, tsohon Ministan tsaron ya bukaci hukumomi su gudanar da bincike na musamman domin ganin an yi adalci.

‘Dan siyasar ya bukaci bincike na gaskiya domin a tabbatar da hakan ya gama aukuwa, jaridar Daily Trust ta kawo rahoton a jiya.

Baya ga bincike wanda tuni shugaban kasa Bola Tinubu ya umarci a fara gudanarwa, Kwankwaso ya nemi a biya diyyar duka rayukan.

Kara karanta wannan

Ba kuskure ba ne: Ahmad Gumi ya dauki zafi a kan kisan masu taron Maulidi a Kaduna

Tsohon gwamnan na Kano yana so gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta biya diyyar jinanen, kuma an ji cewa an yi alkawarin yin hakan.

Jawabin Rabiu Kwankwaso a X

"Na ji takaicin samun labarin dinbin mutanen da aka kashe kuma aka bar wasu sun jikkata da nau’o’in raunuka iri-iri a Tudun Biri a karamar hukumar Igabi.
Sakin bam da ‘kuskure’ wani mummunan aikin jami’an tsaro ne wanda ya yi sanadiyyar hallaka talakawan da ya kamata a ce an ba kariya a kasar nan."

- Rabiu Musa Kwankwaso

Peter Obi da gwamnatin Tinubu

An ji labari Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya yi kaca-kaca da Peter Obi saboda wasu maganganu da ya rika yi a shafinsa.

Idan shugaban kasa ya wanke kan shi daga zargi, sai ‘dan takaran na LP ya sake dauko wani batu, hakan ya jawo aka yi masa dogon raddi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng