Matawalle Ya Dauki Mataki Bayan Kotu Ta Yi Umarnin Kwace Motoci 50 a Hannunsa
- Bello Matawalle bai gamsu da hukuncin da wata babbar kotu ta yi ba kan ƙwace masa motocin alfarma guda 50
- Ministan tsaron ya bayyana hukucin a matsayin rashin adalci tare da garzaya wa kotun ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantarsa
- Matawalle ta hannun lauyansa ya buƙaci kotun da ta jingine hukuncin babbar kotun kan ƙwace masa motocin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Ministan tsaro kuma tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Bello Matawalle, ya garzaya kotun ɗaukaka ƙara domin jingine hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Sokoto ta yi.
Babbar kotun dai ta bayar da umarnin karbo motocin alfarma guda 50 daga hannun tsohon gwamnan. Matawalle ya bayyana hukuncin kotun a matsayin rashin adalci, cewar rahoton Leadership.
A hukuncin da babbar kotun ta yanke ta ce kwato motocin yana cikin tsarin doka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar ƴan sandan jihar ta kutsa cikin gidan Matawalle ne a watan Yuni, jim kaɗan bayan ya bar kujerar gwamnan jihar domin ƙwato motocin da ake zargin na gwamnatin jihar ne.
Meyasa Matawalle ya ɗaukaka ƙara?
Amma ya tunkari babbar kotun ta hannun lauyansa, Dokta Ahmed Raji, SAN, domin ya ƙalubalanci kutsen “ba bisa ƙa’ida ba” da ƴan sanda suka yi a gidansa don ƙwato motocin.
A makon da ya gabata ne dai babbar kotun tayi hukuncin cewa ƙwato motocin yana kan tsarin doka.
Sai dai, saboda rashin gamsuwa da hukuncin, Dr Raji ya shigar da ƙararraki shida na ɗaukaka ƙara, yana mai cewa hukuncin rashin adalci ne.
A cewarsa babbar kotun ta yi kuskure na yanke hukunci bayan ta yi cire shaidun da mai shigar da ƙara da takardun da ya gabatar domin ƙarar.
Ya ƙara da cewa babu wata hujja da ke nuna cewa an nuna wa mazauna gidan umarnin kotu domin shiga kafin ƴan sandan su kutsa su ƙwato motocin.
Wacce buƙata ya nema?
A cewarsa a cikin ɗaukaka ƙarar, babbar kotun ta kasa duba hujjojin da ke gabanta da idon basira kafin ta yanke hukuncin yin watsi da ƙarar Matawalle.
Ya ce hukuncin na kotun ya saɓa wa tarin hujjojin da aka gabatar, inda ya buƙaci kotun ɗaukaka ƙarar da ta amince da ɗaukaka ƙarar tare da soke hukuncin babbar kotun.
Ba a riga an sanya ranar da za a fara sauraron ɗaukaka ƙarar ba.
Matawalle Ya Magantu Kan Tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Bello Matawalle ya bayyana rawar da ya taka a fannin tsaro a ƙasar nan.
Ƙaramin ministan na tsaro ya ce ba don ɗaukar matakin da ya yi a matsayinsa na ɗaya daga jiga-jigan jihar Arewa maso Yamma ba, da dukkanin yankin Arewa ya kama da wuta.
Asali: Legit.ng