Gwamnan Kaduna Ya Dauki Gagarumin Mataki Yayin da Sojoji Suka Sakarwa Masu Maulidi Bam Bisa Kuskure
- Gwamna Uba Sani ya yi martani kan mummunan al'amari da ya faru a kauyen Tudun Biri, inda aka yi kuskure wajen kashe Musulmi a lokacin bikin Mauludi
- Gwamnan ya bayar da umarnin gudanar da binciken gaggawa kan wannan mumunan lamari domin gudun sake aukuwar irin haka a gaba
- Ya kuma roki al’ummar da abin ya shafa da su kwantar da hankalinsu, su kuma ci gaba da baiwa jami’an tsaro goyon baya wajen yaki da ‘yan ta’adda da masu aikata miyagun laifuka
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi umurnin gudanar da cikakken bincike kan harin bam da sojoji suka kai a kauyen Tudun Biri wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka da dama.
Al'ummar kauyen na bikin Maulidi ne lokacin da jirgin sojoji da ke harin yan ta'adda da yan bindiga ya yi kuskuren kashe su tare da jikkata wasu da dama.
A cikin wata sanarwa da ya saki domin yin jaje ga mutanen kauyen Tudun Biri kan wannan mummunan al'amari, gwamnan ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar hana sake afkuwar lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma tabbatar wa al'ummar jihar cewa za a ba da fifiko wajen tsaro da kare su yayin da ake ci gaba da yaki da yan ta'adda, yan bindiga da sauran miyagu.
Uba Sani ya dauki nauyin asibitin wadanda suka jikkata
Yayin da yake umurnin gaggauta kwashe wadanda suka jikkata zuwa asibitin koyarwa na Barau Dikko domin basu kulawa gaggawa, gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna za ta dauki nauyin kula da su da kuma jigilarsu.
Har ila yau, Uba Sani ya roki al'ummar da abun ya shafa da gaba daya mutanen jihar da su kwantar da hankalinsu sannan su ci gaba da ba hukumomin tsaro da gwamnatin jihar goyon baya a yaki da yan ta'adda, yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran miyagu a jihar.
Bugu da kari, ya ce yana tuntubar jami’an tsaro don ganin an kaucewa irin wadannan kura-kurai a ayyukan da za a yi nan gaba.
Pantami ya yi Allah-wadai da kisan yan Maulidi
A gefe guda, Legit Hausa ta rahoto cewa tsohon Ministan sadarwa, Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi Allah wadai da harin da sojoji suka kai wa yan Maulidi bisa kuskure a shafin sada zumunta.
A yayin da ya yi magana a dandalin Twitter, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya nuna akwai bukatar ayi bincike domin a dauki mataki a kai.
Asali: Legit.ng