Yan Bindiga Sun Sace Manyan Attajirai 2 a Abuja, Sun Nemi Makudan Kudin Fansa

Yan Bindiga Sun Sace Manyan Attajirai 2 a Abuja, Sun Nemi Makudan Kudin Fansa

  • Ƴan bindiga sun kutsa cikin birnin tarayya Abuja inda suka sace wasu mutum a yayin wani hari cikin tsakar dare
  • Miyagun ƴan binduga sun shiga cikin unguwar Asokoro inda suka sace wasu mutum biyu masu gidajen haya
  • Ana cigaba da ƙoƙarin ceto mutanen waɗanda tuni ƴan binɗigan suka nemi a kawo musu N20m a matsayin kuɗin fansa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da wasu masu gidajen haya mutum biyu a unguwar Asokoro da ke babban birnin tarayya a ranar Lahadi, 3 ga watan Disamba.

Ƴan bindigan dai na neman a biya su Naira miliyan 20 domin su sako mutanen da suka sace.

Kara karanta wannan

Kaico: An cafke jami'an yan sanda bisa laifin yin garkuwa da mutane da neman kudin fansa

Yan bindiga sun sace mutum biyu a Abuja
Yan bindiga sun sace masu ba da hayar gidaje a Abuja Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Jaridar The Punch ta ce ƴan bindigan ɗauke da makamai sun nuna bindiga a kan daya daga cikin masu gidajen da ke unguwar inda suka yi amfani da shi wajen sace ɗaya daga cikin mutanen da suka ɗauka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya auku

Wani mazaunin unguwar da ya bayyana sunansa James ya bayyana cewa, ɗayan mutumin da aka sace yana kan hanyarsa ta zuwa gidansa ne a lokacin da ƴan bindigan suka yi awon gaba da shi.

A kalamansa:

"Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na daren ranar Lahadi. Saboda zafi ɗaya daga cikin masu gidajen ya kwanta a waje. Suna ganinsa suka nuna masa bindiga a kai. Suka ce ya kai su gidansa, ya nuna musu amma ba su gamsu da irin gidan da yake zaune ba."
"Akwai wasu manyan gidaje kusa da gidansa. Don haka suka tafi tare da shi suka tambaye shi ya kwankwasa ƙofar ɗaya daga cikin gidajen. Da ya kwankwasa, a matsayinsa na sanannen makwabci, aka buɗe masa ƙofa. Ta haka ne suka shiga gidan mutumin suka yi garkuwa da shi."

Kara karanta wannan

Yan sanda sun sheke yan bindiga 50 a yayin wani artabu

"Mai gida na biyu ya samu matsala da motarsa ​​ya zo gida a babur. Yana shirin shiga gidansa sai suka afka masa suka tafi da shi."

Majiyar ya bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan mutanen kuma sun buƙaci a biya su N20m domin su sako su, rahoton The Guardian ya tabbatar.

Wane ƙoƙari jami'an tsaro ke yi?

Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja Josephine Adeh ba, har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Kwamandan Asokoro na ƙungiyar ƴan sakai ta Najeriya, Mohammed Seidu, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ƙara da cewa ana cigaba da ƙoƙari tare da ƴan sanda domin ceto waɗanda lamarin ya ritsa da su.

Ƴan Sanda Sun Sheƙe Ƴan Bindiga 50

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an ƴan sanda da haɗin gwiwar ƴan sakai da sojoji sun sheƙe ƴan bindiga 50 a jihar Taraba.

Jami'an tsaron sun samu nasarar halaka ƴan bindigan ne a wani artabu da suka yi a ƙaramar hukumar Bali ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng