Shugaban Kasar Afrika Ya Hango Abin da Zai Biyo Bayan Cire Tallafin Fetur a Najeriya

Shugaban Kasar Afrika Ya Hango Abin da Zai Biyo Bayan Cire Tallafin Fetur a Najeriya

  • William Ruto ya yabi Bola Ahmed Tinubu a kan yadda ya jajirce wajen yin waje da tsarin biyan tallafin fetur
  • Shugaban Kenya ya shaida cewa cire tallafin mai da aka yi a Najeriya zai kawo cigaba a kasashen da ke Afrika
  • Bola Tinubu da Ruto su na cikin shugabannin kasashen Afrika da su ka halarci taron COP28 a birnin Dubai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Dubai - Shugaban kasar Kenya, William Ruto ya yabi janye tsarin tallafin man fetur da Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya yi a Najeriya.

This Day ta ce Mista William Ruto ya yabawa matakin da takwaransa ya dauka bayan zama shugaban Najeriya a watan Mayun 2023.

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya ya cire tallafin fetur Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Bola Tinubu, Ruto sun je taron COP28

Kara karanta wannan

Abin da yasa Tibunu bai yi jawabinsa ba a taron COP28 kamar yadda aka shirya

Shugaban na Kenya ya bayyana wannan ne da yake jawabi wajen wani taro da shugabannin Afrika su ka yi a birnin Dubai a kasar UAE.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabannin kasashen nahiyar Afrika sun yi wani zama a taron COP28 domin ganin yadda za su shawo kan matsalolin da su ka addabe su.

William Ruto yake cewa ya kamata shugabannin Afrika su rika daukar irin wadannan matsaya masu daci da za su bunkasa tattali.

Kamar yadda The Cable ta rahoto, Shugaba Ruto yana da ra’ayin cewa daina biyan tallafin man fetur da gwamnati tayi, zai taimakawa Afrika.

Yabo ga Tinubu da shugabannin Afrika

“Ina son taya takwarorina, shugabannin kasashe – shugaban kasar Zambiya murna a kan matakan da su ka dauka na gyara tattalin arziki.
Ga Shugaba Tinubu, wanda dole ya dauki mataki mai daci, daga ciki har da cire tallafi.

Kara karanta wannan

Akwai alheri 1: Shugaba Tinubu ya gana da shugaban UAE, hotuna da bayanai sun bayyana

Dole dukkanmu mu dauki wadannan matakai masu wahala domin Afrika ta cigaba, kuma na yi alkawari za mu tsaya tsayin-daka domin daukar matakan da su ka dace domin goben Afrika ta yi kyau."

- William Ruto

Najeriya da Afrika a taron COP28

Ruto ya ce sai an hada-kai da sauran bangarorin duniya domin tunkarar batun sauyin yanayin da yawan kona fetur yana kara jawo shi.

A wajen taron da ake yi a kasar UAE ne aka ji Ruto ya na cewa yanzu kasashe sun fara durowa Afrika domin sun ga irin daman da ake da su.

Tinubu bai yi magana a Dubai ba

Tun tuni sanarwa ta fito cewa Mai girma Bola Ahmed Tinubu zai tafi kasar waje domin halartar taron COP28 game da batun sauyin yanayi.

An ji cewa Shugaban zai gabatar da jawabi gaban kasashen duniya a kan sha’anin sauyin yanayi a Najeriya, amma dai hakan ba ta yiwu ba.

Kara karanta wannan

Bai san ana yi ba, Sanatan APC ya fadi babban kuskuren Buhari a shekaru 8

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng