2019: Ararume, Izunaso sun sauya sheka daga APC zuwa APGA

2019: Ararume, Izunaso sun sauya sheka daga APC zuwa APGA

- Wasu tsofaffin sanatoci daga jihar Imo sun sauya sheka daga jam'iyya mai mulki ta APC zuwa jam'iyyar APGA

- Sanata Ararume shine mai tagomashi a cikin yan takarar gwamnan jihar Imo, yayin da Mrs. Ojukwu zata kara da Mr. Patric a kujera daya

- Yan siyasar guda biyu, na a tsakiyar rikici da gwamnan jihar Imo na yanzu, Owelle Rochas Okorocha

A yayin da guguwar sauyin sheka daga jam'iyya zuwa wata jam'iyyar ke ci gaba da kadawa, musamman a fuskantar zaben 2019 da ke gabatowa, a jiya Laraba, Sanata Ifeanyi Ararume tare da tsohon sakataren tsare tsare na jam'iyyar APC, Sanata Osita Izunaso, sun fice daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar APGA, mai alamar Zakara.

Tsofaffin sanatocin yan asalin jihar Imo, sun cimma wannan matsayar ne bayan da suka kwashe awanni biyu suna ganawa da shugaban jam'iyyar APGA na kasa, Dr. Victor Oye, a sakatariyar jam'iyyar da ke Abuja.

Sanata Ararume shine mai tagomashi a cikin yan takarar gwamnan jihar Imo.

Yan siyasar guda biyu, na a tsakiyar rikici da gwamnan jihar Imo na yanzu, Owelle Rochas Okorocha, sun isa sakatariyar jam'iyyar da ke Abuja don tabbatar da sauya shekarsu daga APC zuwa jam'iyyar ta APGA.

2019: Ararume, Izunaso sun sauya sheka daga APC zuwa APGA
2019: Ararume, Izunaso sun sauya sheka daga APC zuwa APGA
Asali: Instagram

KARANTA WANNAN: Tsare mai laifi sama da awanni 48, hukuncin kora ne - IGP Idris ya gargadi FSARS

A wani labarin, babban dan kasuwa, Mr. Patric Ifeanyi Ubah, wanda shima ya bayyana a sakatariyar jam'iyyar a jiya don sayen tikitin tsayawa takarar majalisar dattijai da zai wakilci mazabar Anambra ta kudu, ya ce ba zai tsaya yana kallo Mrs. Bianca Ojukwu ta kwace masa kujerar ba.

Mrs. Ojukwu itama tana neman tsaya takarar kujerar da Mr. Patric ya ke nema, duka a karkashin jam'iyya daya.

Ya shaidawa manema labarai cewa yana da yakinin samun nasara akan Mrs. Ojukwu a zaben fitar da gwani, don wakiltar al'ummar mazabarsa a majalisar dattijai.

Da aka tambaye shi akan yadda zai iya hada taura biyu a baki daya, ga wakilci ga kasuwanci, musamman ganin cewa bai taba rike wani mukamin siyasa ba, Ubah ya ce yana da kwararrun manajoji da zasu kula da dukkanin harkokin kasuwancinsa, haka zalika yana da kwarewar da zai wakilci al'ummar mazabar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng