Amarya Ta Fasa Aurenta Yayin da Angon Ya Gindaya Mata Sharudda 4 Gabannin Aurensu

Amarya Ta Fasa Aurenta Yayin da Angon Ya Gindaya Mata Sharudda 4 Gabannin Aurensu

  • Wata mai shirin zama amarya ta bayyana sharudda masu ban mamaki da angonta ya gindaya mata a kan aurensu
  • Amaryar ta yi ikirarin cewa angon ya nemi ta shiga kungiyar asiri, ta yi rantsuwa, sannan ta yanke hulda da dukkan abokanta
  • Da Legit ta tuntubi Dexterouz11, ya tabbatar da cewar matar ta dage sai an fasa auren saboda wannan bukata mai ban mamaki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wata yar Najeriya ta nuna damuwa kan bukatu masu ban mamaki da angonta ya nema wata daya kafin bikinsu.

A wasu jerin hira da @dexterouz11 ya wallafa a Twitter, mai shirin zama amaryar ta bayyana cewa yana so ta shiga kungiyar asiri sannan ta yi rantsuwar zama mai gaskiya, tare da zubar jini da mutuwa idan ta ci amanarsa.

Kara karanta wannan

"Nuna mun alama": Budurwa ta ziyarci kabarin mahaifinta, ta nemi ya girgiza bishiya, bidiyon ya yadu

Amarya ta soke aure saboda sharuddan ango
Amarya Ta Soke Aurenta Yayin da Angon Ya Gindaya Mata Sharudda 4 Gabannin Aurensu Hoto: @dexterouz11/NickyLloyd/ Getty Images an yi misali da hoton matar ne
Asali: Twitter

Amarya ta shiga rudani kan bukatun ango gabannin bikinsu

Bugu da kari, matashi ya dace cewa dole ta bar aikinta sannan ta yanke hulda da gaba daya kawayenta kafin su yi aure.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cike da tsananin damuwa kan sharuddan da angon ya gindaya mata, amaryar ta sake nanata shawarar da ta yanke na soke auren.

Ta kara kokawa kan yadda ta fahimci cewaangon nata ba yadda take daukarsa yake ba, kuma ba ta taba tsammanin zai kawo irin wadannan sharudda masu tsauri ba.

Matashiyar da ta karaya ta nanata cewa bata taba ci masa amana ba kuma ba za ta iya shiga rayuwar aure da irin wadannan sharudda ba.

Ta ce:

"Yar'uwa na shafe tsawon shekaru biyar na rayuwata tare da dibia. Ba yadda nake tunani yake ba. Wannan mutumin ya ce zan shiga kungiyar asiri, na yi rantsuwar zama mai gaskiya, idan na yi wani abu na rashin gaskiya na yi ta zubar jini sannan na mutu. Ba zan iya ci gaba da auren ba. Ban taba ganin wannan bangare na nonso ba. A kodayaushe ina kallonsa a matsayin mutumin kirki. Bani da niyan ci masa amana amma bana son shiga wannan.

Kara karanta wannan

Yadda yaran turawa da mahaifinsu suka sharbi kuka a filin jirgi kan rabuwa da mai aikinsu

"Lokacin da ya ce na dauki rantsuwa na zata rantsuwar samun kudi ne. Amma na kawo karshen rayuwara ne, ban taba cin amanarsa ba me zai sa ya yi tunanin wannan. Ba iya wannan ba ya ce na dakatar da aikina sannan na yanke hulda da gaba daya abokaina. Yana fadin wannan ne wata 1 kafin bikinmu. Ban damu ba na fada masa bana yi kuma ya ce zan yi danasani."

Da jaridar Legit ta tuntubi Dexterous11, ya tabbatar da cewar matashiyar ta soke auren.

"Eh ta fasa auren, ya kamata a yi a watan Nuwamba amma ga shi mun shiga Disamba."

Kalli wallafarta a kasa:

Budurwa ta ziyarci kabarin mahaifinta

A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa ta tsuma zukata a TikTok bayan ta yada wani bidiyo na ziyarar da ta kai kabarin mahaifinta.

Matashiyar mai suna @Iromicc a TikTok ta isa kabarin mahaifinta da ya rasu don yin magana da shi amma bata ji amsa daga gare shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng