Ni Na Fatattaki Shekau da Qaqa, Da Yanzu Niger Ta Zama Hedikwatar Boko Haram, Tsogon Gwamna Aliyu
- Tsohon gwamnan Niger ya bayyana kadan daga kokarin da ya yi na wanzar da zaman lafiya a mulkinsa
- Ya ce shi ya fatattaki Shekau da Qaqa daga jiharsa, da yanzu haka Niger ta zama babbar mafakar Boko Haram
- Jihohin Arewacin Najeriya sun fuskanci matsalar tsaro, har yanzu da yawa na ci gaba da fama da matsalar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Niger, Babangida Aliyu, ya bayyana yadda ya fatattaki shugabannin kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau da Abu Qaqa, a lokacin mulkinsa na farko a jihar, inda ya ce da jihar ta zama hedikwatar Boko Haram.
Ya ce wani bangare na magance matsalolin tsaro da suka addabi Najeriya ba komai bane face ta hanyar samar da shiri na musamman don kawo karshen hakan, rahoton The Nation.
A cewarsa, idan za a samu shiri da tsari, za a magance matsalar da ta ingiza yara sama da miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta a halin yanzu.
Aliyu ya bayyana haka ne a Kaduna a karshen mako a lokacin da yake jawabi a matsayin babban bako mai jawabi a taron shekara na Cibiyar Hulda da Jama’a ta Najeriya (NIPR), reshen jihar Kaduna na 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta yaya matsalar tsaro ta fara?
Da yake jawabin yadda ya samu matsalar tsaro a jiharsa lokacin da yake gwamna, Daily Trust ta naqalto shi yana cewa:
“Kasancewa jajirtacce a matsayin jagora kuma mabiyi shima ya taimaka sosai. A lokacin da na zo gwamna a jihar Niger, na samu kalubalen tsaro ta hanyar wasu mutane tara da suka addabi wani kauye a karamar hukumar Mokwa, wadanda suka rubanya a 2007 zuwa mutum 7,000 kuma suna fashi da makami da sace mata a yankin. Sun maida kansu wata jamhuriya.”
Yadda na shawo kan lamarin, inji Aliyu
A jawabinsa na yadda ya shawo kan matsalar tsaro, tsohon gwamnan ya bayyana cewa:
“Lokacin da na yi kidaya, na gano cewa sama da 60% na ‘yan ta’addan ba ’yan Najeriya ba ne. Asali Shekau da Abu Qaga su ne shugabanninsu.
“Na samu goyon bayan Marigayi Shugaban Kasa Musa Yar’adua na tarwatsa su bayan an biya su diyya tare da samar musu da abin hawa zuwa inda suka fito a Najeriya sannan aka kai ‘yan kasashen waje iyakokin kasa.”
Yadda aka kashe Shekau
A wani labarin, wasu da ake zargin 'yan ISWAP ne a ranar Laraba sun kashe shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, yayin wani kazamin fada a maboyar su ta Dajin Sambisa. In ji wata majiya da ba a tabbatar ba, Vanguard ta ruwaito.
Gandun dajin Sambisa yana da iyaka da kananan hukumomin Konduga, Bama, Gwoza Askira Uba, Hawul, Kaga da Biu a kananan hukumomin Borno, tare da wasu yankuna na Gujuba, Buni Yadi, Goniri a Yobe da Madagali a jihar Adamawa.
Wasu majiyoyi sun ce daruruwan mayakan ISWAP sun mamaye Sambisa da motoci dauke da manyan bindigogi da ke farautar Shekau wanda shi ne shugaban kungiyar Boko Haram.
Asali: Legit.ng