Kungiyar ta'addanci ta ISWAP ta bayyana dalilin da yasa ta kashe Shekau har lahira

Kungiyar ta'addanci ta ISWAP ta bayyana dalilin da yasa ta kashe Shekau har lahira

- Kungiyar ISWAP ta sanar da cewa ta halaka Shekau ne saboda kwarewarsa a ta'addanci, kashe jama'a babu dalili da rashawa

- Kamar yadda Abu Mus'ab Albarnawi, shugaban ISWAP ya sanar, sun samu umarnin kashe Shekau ne daga shugaban ISIS

- Albarnawi ya bayyana yadda Shekau ya kashe kansa ta hanyar tada bam dake jikinsa bayan mayakan ISWAP sun cafke shi

Kungiyar ta'addanci ta ISWAP ta bayyana dalilinta na kashe shugaban kungiyar ta'addanci ta Boko Haram, Abubakar Shekau, Daily Nigerian ta ruwaito.

A wani sakon cikin gida daga shugaban ISWAP, Abu Musab Albarnawi, wanda jaridar HumAngle ta samu a ranar Juma'a, ya ce Shekau ya kashe kansa ne bayan kin mika kai da yayi sakamakon kutsen da aka yi a maboyarsu a ranar 19 ga watan Mayun 2021.

KU KARANTA: Bidiyon mutumin da ya dako tsalle daga jirgin sama babu kumbo, ya kafa tarihi a duniya

Kungiyar ta'addanci ta ISWAP ta bayyana dalilin da yasa ta kashe Shekau
Kungiyar ta'addanci ta ISWAP ta bayyana dalilin da yasa ta kashe Shekau. Hoto daga @HumAngle
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan bindiga 5 sun hadu da ajalinsu bayan sun yi arangama da 'yan sanda a Katsina

Shugaban ISWAP yace shugaban rikon kwarya na ISIS na Iraq da Syria ya bada umarnin su dauka mataki kan Shekau saboda bijire musu da kuma kashe "masu imani" da yake yi.

Kamar yadda yace, Shekau wanda ya karba ragamar Boko Haram bayan mutuwar Mohammed Yusuf a 2009, an kama shi a yanayi mai matukar tozarci.

"Wannan mutum ne da ya dinga ta'addanci. Mutane nawa ya salwantar? Mutane nawa ya halaka? Amma Allah ya bar shi tare da bashi tsawon rayuwa.

"A yayin da lokaci yayi, Allah ya ba sojojinmu nasara bayan sun karba umarni daga shugaban muminai," yace.

Da farko ya gudu kuma ya fara yawo a dajikan Sambisa na kwanaki biyar inda ya sha matukar wahala.

Amma kuma mayakan ISWAP sun yi kokarin nemo shi. Har ila yau Abu Mus'ab ya bada labarin yadda Shekau ya sake tserewa a karo na biyu amma suka bi shi tare da kama shi.

Mayakan ta'addancin sun yi kira gareshi da magoya bayansa da su tuba, tare da tabbatar masa da cewa idan shugaban ISIS ya yanke hukuncin shugabantar da shi a kansu, basu da wani zabi da ya wuce biyayya garesa.

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Ribas ta cafke wata kungiyar 'yan fashi da makami ta mutum uku da suka kware wurin fashi ga jama'a a wuraren Choba/Obiri dake Ikwerre a jihar.

An kama su ne bayan nasarar da suka samu wurin fashi ga wani Simon Ibrahim wanda ke kan hanyarsa ta zuwa banki zuba kudi. Kungiyar ta tare shi yayin da yake tuka motarsa kirar Mazda.

Amma kuma sa'a ta kubuce musu yayin da wanda suka tare din ya kira 'yan sanda kuma aka kama su a take tare da kaisu ofishin 'yan sanda dake Choba, Channels TV ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel