ASUU Ta Tubure, Ta Ce Bata Amince a Ba Dalibai Rance Ba, GA Abin da Take So a Yi
- ASUU reshen jihar Bauchi ta ce bai dace gwamnatin Tinubu ta kawo shirin ba dalibai rancen kudi don yin karatun digiri ba a kasar nan
- Ta ce kamata ya yi a ce gwamnati ta kawo shirin ba dalibai tallafin karatu don karfafa musu da kuma yin kokari a karatunsu
- An kawo shirin ba dalibai rance a shekarar nan, ana ta cece-kuce da bayyana ra’ayoyi kan yadda shirin zai kasance
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
Jihar Bauchi - Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) reshen jihar Bauchi, ta jaddada kudirinta na kin amincewa da ba dalibai rancen tare da neman a ba su tallafin karatu, Daily Trust ta ruwaito.
Ko’odinetan kungiyar ASUU na shiyyar Bauchi, Farfesa Lazarus Maigoro ne ya bayyana haka a jiya a wajen bikin bayar da tallafin karatu ga dalibai marasa galihu 19 da ke shiyyar a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi.
Matsayar shugaban ASUU a Bauchi
Farfesa Maigoro ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Tambayar ita ce: Wa zai biya bashin? Menene makomar wadanda ba za su iya samu ba? Tashin hankalin da dalibai za a fuskanta saboda bashi yayin da suke kan karatunsu zai shafi kyawun sakamakonsu.
"Tunanin cewa za su kammala karatunsu da bashin Naira miliyan 4 ko sama da haka ba tare da ikon biya ba, wani azabtar da tunani ne a kansu."
Tallafi za a ba dalibai ba rance ba
Ya ce ASUU a jihar Bauchi na kokarin ganin an samu kididdigar daliban da za su daina karatu a karshen wannan zangon, tare da fatan gwamnati ta sake duba matakin da ta dauka kan batun ba dalibai rance tare da kawo hanyar tallafa musu, Tribune Online ta tattaro.
Tun da farko a jawabinsa na maraba, shugaban ASUU a ATBU, Kwamared Ibrahim Inuwa, ya ba da tabbacin cewa ASUU za ta ci gaba da kasancewa kungiyar da za ta ke fafutuka don kare muradan dalibai a Najeriya.
Duk shekara ake ba dalibai tallafi a ATBU
Ya jaddada cewa ba da tallafin karatun da aka yi, wanda yace ana yi shekara-shekara, za a rika neman hazikan dalibai amma marasa galihu domin karramawa da shajja’a su.
Wasu daga cikin daliban da suka ci gajiyar shirin sun yabawa ASUU bisa wannan karimcin, inda suka ce idan ba a basu tallafin ba, tabbas za su daina karatu.
Jami'o'i sun kara kudin makaranta
A wani yanayi mai ban tsoro, Shugaban kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan dokar bayar da bashi ga dalibai a cikin satinsa na farko akan mulki, hakan ya sanya aka kara kudin makaranta a kasar nan.
Wahalar da iyaye da dalibai ke daukar nauyin karatunsu su ke sha ta ninka sosai bayan an tsige tallafin man fetur da dakatar da mabambantan farashin canjin dala.
Asali: Legit.ng