Albashi Mai Tsoka: Kasar Singapore Na Neman Ma’aikata Daga Waje, Har Da ’Yan Najeriya

Albashi Mai Tsoka: Kasar Singapore Na Neman Ma’aikata Daga Waje, Har Da ’Yan Najeriya

  • Kasar Singapore na neman ma'aikata daga sassa daban-daban a fadin duniya su cike gibin aiki a kasar
  • An ba da rahoton cewa, kasar ta rasa ma'aikatan kasashen waje 194,000 sakamakon barkewar annoba
  • Kasar ta fara farfadowa daga asarar da ta yi, amma tana bukatar karin ma'aikata domin cike gibin aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Sakamakon raguwar ma'aikata a fannin fasaha, Singapore tana gayyatar kwararru 260,000 don cike gibin ma’aikinta.

Yayin da take fuskantar karancin ma’aikata, kasar na bukatar habaka karfin ma'aikata don cike gibi a fannin IT da zubin na’ura, banki, da aikin injiniya.

Singapore na neman ma'aikata
Ana neman ma'aikata a kasar Singapore | Hoto: aro Hama @ e-kamakura, Pixdeluxe
Asali: Getty Images

Wani rahoton fasaha ya nuna cewa, wannan wani bangare ne na kokarin da take yi na magance illar ficewar ma’aikatan kasashen waje da annoba ta haifar da ya kai ga rasa ma’aikata sama da 194,000.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya kunno PDP yayin da Atiku da fitaccen gwamna suke neman iko, karin bayani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, an gano cewa, tsarin biza na aiki a kasar da kuma ayyukan da za a bayar sun kai ga a biya mutum sama da $3,600 a duk wata guda.

Kididdiga daga bayanan kasar

Bayanai na baya-bayan nan sun gano cewa, yawan jama'ar Singapore ya karu da 5% a cikin shekara guda yayin da ma'aikatan ketare suka dawo birnin bayan barkewar annobar Korona.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, yawan al’ummar LASAR ya karu daga miliyan 5.6 a watan Yunin bara zuwa miliyan 5.9 a watan Yunin 2023.

Adadin ya nuna cewa 30% 'yan kasashen waje ne da ke aiki ko zaman karatu a a Singapore, 9% mazaunan dindindin ne, yayin da 61% kuma 'yan asalin Singapore ne.

Ma’aikatan da ake nema a halin yanzu

Fannonin da ake neman ma’aikata sun hada da sashe da yawa na injiniyanci, harkar na’ura da dai sauransu, ga su kamar haka:

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji sun kakkabe 'yan ta'adda 180 tare da kubutar da mutum 234

  1. Software Developers
  2. Data Scientists
  3. Cybersecurity Experts
  4. Artificial Intelligence Specialists
  5. Fintech Professionals
  6. IT Infrastructure Engineers
  7. Project Managers

Har yanzu ana ta batun yaji a Najeriya

A Najeriya kuma, Ministan Kwadago da Ayyuka, Simon Lalong ya gayyaci Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) wata ganawa don dakile shirinsu na shiga yajin aiki.

Daraktan yada labarai na ma’aikatar, Olajide Oshundun shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a yau Lahadi 17 ga watann Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.