Tinubu Ya Warewa Buhari, Osinbajo da Jonathan Naira Biliyan 13 a Kasafin Kudin 2024
- Tsofaffin shugabannin kasa na mulkin farar hula da sojoji su na da kaso a kasafin kudin shekarar 2024
- Gwamnatin Bola Tinubu za ta batar da biliyoyi a kan shugabannin kasar da su ka yi mulki da mataimakansu
- Jami’an da su ka kai matsayin shugabannin hukumomi da ma’aikatun Gwamnatin Tarayya za su samu N10bn
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Gwamnatin tarayya ta ware N13,805,814,220 domin dawainiyar tsofaffin shugabanni da mataimakansu da aka yi a kasar nan.
Punch ta ce shugabannin kasa da mataimakansu da aka yi a lokacin mulkin soja har zuwa mulkin farar hula za su amfana da wadannan kudi.
Sauran wadanda za a biya alawus daga kason su ne tsofaffin shugabannin ma’aikata da manyan sakatarorin gwamnatin tarayya masu ritaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami’an da su ka rike shugabancin hukumomi, cibiyoyi da ma’aikatun gwamnatin tarayya za su samu kasonsu a cikin kasafin kudin na 2024.
Za a biya Obasanjo, Jonathan da Buhari a kasafn kudi
A shugabannin fararen hula gwamnatin tarayya za ta biya alawus ga Olusegun Obasanjo, Dr. Goodluck Jonathan da kuma Muhammadu Buhari.
Haka akwai Alhaji Atiku Abubakar, Arch. Namadi Sambo da Farfesa Yemi Osinbajo.
Tsofaffin shugabannin soji da aka ware kudin da su sun kunshi; Janar Yakubu Gowon, Janar Abdusalami Abubakar da Janar Ibrahim Babangida.
Air Commodore Ebitu Ukiwe (retd.). wanda ya yi wa Babangida mataimaki ya na cikinsu. Irinsu Janar Oladipo Diya da Tunde Idiagbon duk sun rasu.
Karin albashi a kasafin kudin 2024
Shugabannin kasa za su tashi da N2.3bn sai N11.5bn za su tafi ga tsofaffin shugabannin hukumomi da manyan sakatarori da su ka yi ritaya.
Daily Post ta ce an ware N1tr domin a iya sallamar ma’aikatan da aka yi wa karin albashi.
Yadda ake biyan tsofaffin shugabanni
Ba wannan ne karon farko da aka biya tsofaffin shugabanni, a kan yi masu tanadin alawus na musamman da zai iya kula da su bayan barin ofis.
Da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kasafin N16tr a 2022, tsofaffin Shugabanni da Ma’aikatan Gwamnati sun lamushe Biliyoyin kudi a shekarar.
Asali: Legit.ng