Zargin Maita: An Shiga Tashin Hankali Bayan Matashi Ya Aika Kawunsa Lahira, Ya Yi Bayani
- Kotun majistare da ke jihar Adamawa ta tasa keyar wani matashi zuwa gidan kaso kan zargin hallaka kawunsa
- Ana zargin John Clarkson da kisan kawunsa kan zargin maita a kauyen Dumna Zarbu a karamar hukumar Guyuk
- Bayan sauraran kararrakin, Mai Shari'a, Alheri Ishaku ta dage ci gaba da sauraran shari'ar har sai ranar 4 ga watan Janairun 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Adamawa - Kotun majistare ta tasa keyar wani matashi zuwa gidan gyaran hali kan zargin yin ajalin kawunsa a jihar Adamawa.
Wanda ake zargin mai suna John Clarkson mai shekaru 42 ya hallaka kawun nasa ne kan zargin maita, Leadership ta tattaro.
Wane hukunci kotun ta yanke a jihar Adamawa?
Kotun majistare da ke Yola karkashin jagorancin Mai Shari'a, Alheri Ishaku ita ta yanke wannan hukunci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ta umarci tsare Clarkson dan asalin kauyen Dumna Zarbu da ke karamar hukumar Guyuk a jihar.
Bayan ba da umarnin ci gaba da tsare shi, Mai Shari'a, Alheri ta dage ci gaba da sauraran shari'ar har sai ranar 4 ga watan Janairun 2024.
Wane zargi ake kan Clarkson a Adamawa?
Yayin tasa keyar tasa, wanda ake zargin ya musanta kisan kawun nasa kan zargin maita.
Marigayin da ake zargin dan nasa ya kashe shi mai suna Mohammed Clarkson, John na zarginshi da kisan mutane ta hanyar maita.
Ana zargin John ya yi wa marigayin dukan tsiya da sanda har sai da ya yi ajalinsa.
Wannan danyen hukunci ya sabawa dokokin laifuka na sashi 191 na kundin laifukan jihar Adamawa.
Zargin maita a Najeriya ya zama ruwan dare inda a shekarun baya wani mahaifi ya cinna wa 'ya'yansa biyu wuta a jihar Plateau.
Kotu ta yi hukunci a shari'ar Abba Kabir da Doguwa
A wani labarin, Kotun Daukaka Kara ta yi kori karar Gwamna Abba Kabir na jihar Kano kan zargin ta'addanci da ya ke yi wa Ado Doguwa.
Abba na zargin dan Majalisar da jagorantar 'yan ta'adda tare da cinna wa sakatariyar jam'iyyar NNPP wuta a watan Faburairu.
Sai dai kotun, yayin hukuncinta, ta umarci gwamnan da ya biya naira miliyan 25 kudin diyya.
Asali: Legit.ng