Zargin maita: Mahaifi ya bankawa 'ya'yansa biyu wuta

Zargin maita: Mahaifi ya bankawa 'ya'yansa biyu wuta

Hukumar 'yan sandan jihar Filato ta tabbatar da yadda wani mahaifi ya bankawa 'ya'yansa biyu wuta, bayan da ya zargesu da maita. Nyam Choji dan asalin kauyen Shen ne dake karamar hukumar Jos ta Kudu.

Ya bankawa 'ya'yansa biyu wuta bayan da ya zargesu da maita.

Mukaddashin kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Uba Gabriel, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Lahadi ga jaridar Daily Trust. Sunayen yaran shine Godsgift Nyam mai shekaru 11 a duniya da Mary Nyam mai shekaru 11.

Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma'a. "Daga bayanan da muka samu, mahaifin yaran da 'ya'yan mai Anguwar yankin sun kasance suna wannan harkar a yankin. Suna nan da yawa, mun sa a bankado mana su a yankin," in ji shi.

DUBA WANNAN: Karar kwana: Yadda Amarya da 'yan rakiyarta 21 suka mutu a hatsarin mota

Kamar yadda 'yan sandan suka sanar, an kwantar da yaran a asibitin kwararru na Jos.

A mayar da martanin gaggawa a kan wannan cigaban, kungiyar manema labarai mata ta Najeriya (NAWOJ), a wata takarda da shugabarta ta saka hannu, Jennifer Yarima, ta kushe wannan lamarin. Ta kwatanta hakan da take hakkin kananan yara.

Hukumar tayi kira ga Gwamna Simon Bako Lalong da ya bibiyi lamarin tare da tabbatar da anyi wa yaran adalci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng