Daraktan DSS, Bichi Ya Handame Kudaden Tallafin Ma'aikatansa? Gaskiya Ta Bayyana
- An zargi daraktan hukumar DSS, Yusuf Bichi da handame kudaden ma'aikata na rage radadi
- Sai dai hukumar ta karyata labarin wanda wani Jackson Ude ya wallafa a shafinsa na Twitter
- Daraktan yada labarai na hukumar, Dakta Peter Afunanya shi ya bayyana haka a yau Asabar 2 ga watan Disamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Hukumar DSS ta yi fatali da jita-jitar cewa daraktan hukumar, Alhaji Yusuf Bichi ya handame kudaden rage radadi na ma'aikata.
Wani mutum mai suna Jackson Ude shi ya yi wannan zargi inda ya ce Bichi ya yi sama da fadi da tallafin kudaden ma'aikatan hukumar.
Wane zargi ake yi kan daraktan DSS, Bichi?
Daraktan yada labarai na hukumar, Dakta Peter Afunanya shi ya yi wannan martani a yau Asabar 2 ga watan Disamba a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Afunanya ya ce Ude a kullum kokarin bata sunan Bichi ya ke a matsayin mai cin hanci da rashawa inda hukumar karyata.
Ya ce hukumar ta yi bincike a baya kan irin wadannan zarge-zarge inda ta tabbatar karairayi ake yi wa Bichi, The Nation ta tattaro.
Mene martanin DSS kan zargin Bichi da cin hanci?
Sanarwar ta ce:
"Hukumar DSS ta samu labarin zargin cin hanci kan Bichi da wani Jackson Ude ya wallafa a shafinsa na Twitter.
"Hukumar ta tabbatar da wannan magana karya ce kuma babu wani daga cikin ma'aikatanta da ya handame kudaden tallafi.
"Babu wasu kudaden tallafi da aka turo wa hukumar kuma da zarar an turo kowa zai samu kasonshi kamar yadda aka saba."
Afunanya ya ce Bichi ba irin wannan mutumin ba ne saboda ya damu da walwalar ma'aikatansa har da wadanda su ka yi ritaya, cewar Platinum Post.
Da gaske Gwamna Caleb na nuna wariya ga Musulmai?
A wani labarin, Al'ummar Musulmai a jihar Plateau sun bayyana alakarsu da Gwamna Caleb Mutfwang.
Kungiyar ta ce gwamnan ya na kokari wurin tabbatar da adalci a yayin raba mukamai.
Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin nuna wariya ga al'ummar Musulmai a jihar.
Asali: Legit.ng