“Budurwar Wani”: An Kama Budurwa Tana Wawure Kudin Ango da Amarya a Wajen Biki, Bidiyo Ya Bayyana

“Budurwar Wani”: An Kama Budurwa Tana Wawure Kudin Ango da Amarya a Wajen Biki, Bidiyo Ya Bayyana

  • Jama'a sun yi cece-kuce kan bidiyon wata matashiyar budurwa da aka nada yayin da take wawure kudi daga wata jaka da ta rikewa wasu ma'aurata
  • Mutumin da ya kama ta a kamara ya yi ikirarin cewa tana taimakawa amarya da angon ne wajen tattara kudaden da mutane suka lika masu
  • Yayin da mutane da dama suka caccaiki matashiyar kan abun da ta aiakata, wasu mutane sun goyi bayanta cewa koda su ne abun da za su yi kenan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Wani bidiyo da ke yawo ya hasko wata matashiyar budurwa da aka dauka tana wawure kudin liki da ya kamata ace tana taya amarya da ango kwashewa.

Wani dan TikTok, @preshkc1, wanda ya yada bidiyon a dandalin soshiyal midiya ya ce:

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya raba daloli a unguwa, Kirkinsa ya tsorata mata, sun tsere a bidiyo

"Wannan ne dalilin da yasa nake sa hannuna na kwashe kudina."
Budurwa ta wawure kudin likin amarya da ango
“Budurwar Wani”: An Kama Budurwa Tana Wawure Kudin Ango da Amarya a Wajen Biki, Bidiyo Ya Bayyana Hoto: Roberto Westbrook, TikTok/@preshkc1
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jawabin da ke kan bidiyon ya yi bayanin cewa matashiyar na taya amarya da angon kwashe kudaden da mutane suka lika masu ne lokacin da ta yi masu gibi.

A bidiyon, ta rike wata yar jaka da ke kunshe da kudin sannan ta gaggauta turmutsa hannunta a ciki don taimakon kanta da yan wasu kudade.

Ta boye shi a cikin wata yar jaka da ke kugunta.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani kan bidiyon

user5227312281188 ya ce:

"Abun da suka yi mani kenan a ranar aurenmu...amma na bar abun a hannun Allah."

D Wyze1 Comedy ya ce:

"Budurwar wani kenan fah...Kuma wani gaye na nan ya mato kan soyayyar."

QUEEN PERRY ta ce:

"Ranar aurena kana daukar kudi a taron za ka gabatar mani nan take idanuna na ta yawo ne a ko'ina musamman kan kudi."

Kara karanta wannan

Kamar almara: Matar aure ta datse igiyar aurenta na wata 6, bidiyon ya jawo muhawara

lady j. ta ce:

"Ba sabon abu bane nima yi zanyi ku huta don Allah ku da kuke magana za ku fi kowa yi."

derin hair-institute ta ce:

"Dukkanku za ku iya yin wannan, harda wanda ya wallafa bidiyon nan."

Jarumar Kannywood ta ba da hakuri

A wani labari na daban, mun ji cewa fitacciyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Khadija Kabir Ahmad, wacce aka fi sani da Khadija Mai Numfashi, ta yi martani bayan dakatar da ita da hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta yi.

Shugaban hukumar tace fina-finai, Abba Al-Mustapha ya sanar da haramtawa jarumar shiga duk harkokin masana’antar, bayan an dakatar da ita na tsawon shekaru biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng