Matashi Dan Shekaru 20 Ya Auri Matashiyar Budurwa, Bidiyon Aurensu Ya Haddasa Cece-kuce A Intanet

Matashi Dan Shekaru 20 Ya Auri Matashiyar Budurwa, Bidiyon Aurensu Ya Haddasa Cece-kuce A Intanet

  • Wani matashin dan Najeriya mai shekaru 20 ya je shafin soshiyal midiya don nuna shagalin aurensa da kyakyyawar matarsa
  • A cewar matashin wanda ya kasance jinin sarauta, aurensa ya cancanci shiga kundin tarihi na duniya
  • Bidiyon auren sabbin ma’auratan wanda aka yi a 2022 ya haifar da martani a shafukan intanet

Wani matashin dan Najeriya mai shekaru 20 ya wallafa bidiyon aurensa da wata yarinya da yayi ikirarin shekarunta 17.

Matashin ya yi alfahari da kasancewarsu ma’aurata mafi karancin shekaru, yana mai cewa sun cancanci shiga kundin tarihu na duniya.

Ma'aurata
Matashi Dan Shekaru 20 Ya Auri Matashiyar Budurwa, Bidiyon Aurensu Ya Haddasa Cece-kuce A Intanet Hoto: TikTok/@apito.luxury
Asali: UGC

Ya wallafa wani bidiyon shagalin bikinsu wanda aka yi a wata jiha da ke yankin kudu maso gabashin kasar a TikTok.

An gano matashin wanda ya kasance jinin sarauta yana rawa yayin da baki da masu fatan alkhairi key i masa yayyafin kudi.

Kara karanta wannan

Tsagerun Yan Bindiga Sun Kashe Sojoji 5 Da Dan Farar Hula Daya A Anambra

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wani bangaren, ma’auratan sun tsuguna don samun tabarraki daga wajen iyayensu.

Bidiyon aurensu ya haddasa cece-kuce a shafukan soshiyal midiya.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani

Nnenna♥️ ta ce:

“Idan kayi aure kana karami ko bayan ka tsufa babu tabbacin cewa zai dade. Yawancin mutane na tunanin auren wuri takura ne saboda suna tsoron jajircewa. Ka ji dadinka dan uwa.”

user7340942123326 ya ce:

"Ina maka fatan farin ciki a rayuwar aurenka, tsawon rai, yalwa da lafiya mai inganci, farin ciki soyayya mai dorewa da yara tabbass ne.”

banny ta ce:

“Yana faruwa yar’uwata tayi aure tana da shekaru 16 mijinta ke kula da karatunta yanzu yaranta uku.”

Kirirkiristar ta ce:

“Ba zai taba faruwa a kaina ko diyata ba kwata-kwata dole sai ta san abubuwa game da rayuwa.”

Tashi Ka Nemi Abun Yi: Fusatattar Matar Aure Ta Dangwararwa Da Miji Kwano Babu Abinci

Kara karanta wannan

Matashiya Ta Fashe Da Kuka Yayin da Aka Yi Mata Kwalkwabo Bayan Mutuwar Mijinta, Bidiyon Ya Taba Zukata

A wani labarin, masu amfani da TikTok sun yi martani ga wani bidiyo na wata mata da ta gabatarwa mijinta kwano wayam babu abinci a ciki.

A cikin bidiyon, mutumin ya zauna yana jiran a kawo masa abincinsa, kawai sai gashi an dangwaran masa da kwano babu komai.

A cewar matar, mutumin bai da wani aiki sai na tambayar abinci ba tare da fita aiki ko kawo gudunmawar komai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel