Fitaccen Sarki a Arewa Ya Raba Zakkah Ga Talakawa Marasa Galihu 10,000, An Bayyana Miliyoyin Kuɗin
- Sarkin Kazaure a jihar Jigawa, Dakta Najib Hussaini Adamu, ya raba zakka da ta kai N60m ga maɓukatan da suka cancanta
- Kwamitin tattara zakkah da rabawa na masarautar ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar bayan kammala rabon
- Shugaban kwamitin, Alhaji Bala Muhammad, ya faɗi rukunin mutanen da suka amfana wanda a jimulla sun kai 10,000
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Jigawa - Mai Martaba Sarkin Kazaure, Dakta Najib Hussaini Adamu, ta hannun kwamitin Zakka na Masarautarsa, ya raba zakkah ta tsabar kudi da hatsi ga mabuƙata.
Sarkin ya raba wannan Zakkah da ta kai kimanin Naira miliyan 60 ga mabuƙata 10,000 waɗanda addinin Musulunci ya yi umarnin a ba su zakkah, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da masarautar Kazaure da ke Jigawa ta fitar bayan kammala aikin rabon mai ɗauke da sa hannun shugaban kwamitin, Alhaji Bala Muhammad.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Muhammad ya bayyana cewa an gudanar da rabon ne a yankin hakimai 10 da ke a ƙarƙashin masarautar bayan lissafa tare da tantance sunayen wadanda suka ci gajiyar kuɗin Zakkah.
Su wa aka rabawa Zakka?
Ya kara da cewa wadanda suka ci gajiyar sun hada da magidanta masu ƙaramin ƙarfi, zawarawa, marayu, masu tabin hankali, nakasassu da sauran marasa galihu a cikin al’umma.
A rahoton jaridar Guardian, shugaban kwamitin ya ce:
“Har ila yau, daga cikin wadanda suka amfana akwai wadanda ke bukatar ƴan kudi don farawa ko ci gaba da kananan sana’o’insu, wadanda su ne hanyar samun kuɗin shigarsu tsawon shekaru."
"Bugu da ƙari marasa lafiya da suka gaza biyan kuɗin magani na daga cikin waɗanda aka talllafa wa da kuɗin Zakkar."
Ya ci gaba da cewa ana karbar zakka ne daga manoma da masu hannu da shuni a masarautar kana a raba su kamar yadda Allah SWT ya umarta a cikin Alkur’ani mai girma.
"Muna kira ga sauran masu hannu da shuni da su bada zakkarsu ta wannan kwamiti mai tsari domin rabawa wadanda suka dace ta hanyar da ta dace,” inji shi.
Gwamna Lawal ya bankado wani bashi da ake bin Zamfara
A wani rahoton kuma Gwamna Dauda Lawal ya bayyana makudan kuɗin da ma'aikatan da suka yi ritaya suka biyo gwamnatin Zamfara bashi.
Ya ce bayan hawansa kan madafun iko ya ɗauki matakai kuma ya yi alkawarin fara biyan gratuti da alawus din yan fansho.
Asali: Legit.ng