Jami'an Tsaro Sun Cafke Babban Shugaban Yan Ta'addan ISWAP, Bayanai Sun Fito
- An samu nasarar rage mugun iri bayan an cafke shugaban ƴan ta'addan ISWAP mai kula da shiyyar Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Gabas
- Shugaban ƴan ta'addan ya shiga hannu ne a wani sumamen haɗin gwiwa da sojoji da jami'an DSS suka kai
- Dakarun sojojin sun kuma yi luguden wuta a maɓoyar shugabannin ƴan ta'addan a shiyyar Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Gabas
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Dakarun sojoji tare da haɗin gwiwar jami'an rundunar ƴan sandan fararen kaya (DSS), sun cafke shugaban ƙungiyar ƴan ta'addan ISWAP na shiyyar Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma.
Ko da yake rundunar ba ta bayyana sunan shugaban ƴan ta'addan ba, amma ta ce yana tsare, cewar rahoton The Punch.
A wata sanarwa a ranar Juma’a da Daraktan yada labarai na rundunar tsaro, Manjo Janar Edward Buba, ya fitar, ya ce ƙudurin da sojoji suka yi na bin shugabannin ƙungiyoyin ƴan ta’addan ne ya kai ga cafke shugaban ƴan ta'addan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun ragargaji ƴan ta'adda
Ya yi nuni da cewa, hare-haren da aka kai ta sama da aka gudanar a yankunan ya kai ga lalata maɓoyar ƴan ta'addan.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Ayyukan da sojoji ke cigaba da yi na cigaba da lalata rundunonin ƴan ta'adda, masu laifi da kuma masu tayar da ƙayar baya a faɗin ƙasar nan. Don haka, ƙarfin faɗansu ya ragu sosai kuma sun gudu."
"Sojoji suna farmakar shugabannin waɗannan ƙungiyoyin ne domin tabbatar da cewa ba su ƙara yin barazana ga tsaro da zaman lafiyan jama'a ba."
"A ranar 29 ga watan Nuwamba, a ƙauyen Tarum da ke wajen babban birnin Bauchi a jihar Bauchi, sojoji sun haɗa kai da jami’an DSS wajen gudanar da wani samame, wanda ya kai ga kama shugaban ƙungiyar ta’addanci ta ISWAP mai kula da shiyyar Arewa ta tsakiya da shiyyar Arewa maso Yamma."
"Yana tsare. Hakazalika, an kai hare-hare ta sama a yankuna da dama na waɗannan shugabannin ƴan ta'adda a shiyyar NW da NC tare da samun nasara."
Jami'an Tsaro Sun Sheke Ɗan Bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an rundunar ƴan sandan Najeriya sun samu nasarar sheƙe wani ɗan bindiga a jihar Bauchi a yayin wani artabu.
Jami'an ƴan sandan sun kuma samu nasarar ceto wasu mutun uku da ƴan bindigan suka yi garkuwa da su.
Asali: Legit.ng