Babu Komai a Kwalayen Kasafin Kudin da Shugaba Tinubu Ya Kawo – ‘Dan Majalisar NNPP
- Shugaba kasa ya gabatar da kasafin kudi, amma an samu wasu ‘yan majalisa da ke zargin cewa yaudararsu kurum aka yi
- Wani ‘dan majalisa ya ce babu abin da ke cikin akwatin da Bola Ahmed Tinubu ya mika masu, kuma ana neman rufe maganar
- Hon Yusuf Shitu Galambi mai wakiltar Gwaram ya zargi shugaba Tinubu da garajen kawo kundin da ba a gama aikinsa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja- Kasafin kudin da Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya gabatar gaban ‘yan majalisar tarayya ya jawo abin magana a Najeriya.
Kwanaki da mikawa ‘yan majalisa kundin kasafin kudin shekara mai zuwa, BBC Hausa ta rahoto cewa ana zargin duk dodo-rido ce.
Da aka yi hira da Yusuf Shitu Galambi, ya shaida cewa babu abin da su ka samu a cikin kwalayen da shugaban Najeriya ya kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babu komai a kundin kasafin Tinubu
‘Dan majalisar na Gwaram ya zargi shugaban kasa Bola Tinubu da garaje domin ya ce babu abin da su ka iya samu na bayanan kudin.
Honarabul Yusuf Shitu Galambi ya fadawa BBC, manyan majalisa su na ta kokarin yin rufa-rufa, ba su so a bar maganar ta bar majalisar.
Galambi yake cewa a tarihin majalisa, wannan ne karon farko da shugaba zai kawo masu kasafin kudin kasa da babu komai a cikinsa.
Idan maganar ‘dan majalisar na NNPP ta tabbata, babu wani bayani dauke da kudin da aka warewa kowace ma’aikata a kasafin na 2024.
Kasafin kudi: Hon. Galambi ya ce abin da mamaki
“Mu kanmu 'yan majalisar wannan abin ya daure mana kai, saboda abu ne wanda ba a taba gani ba.
Mun duba kundin da ya ajiye amma ba mu ga komai a cikinsa ba."
- Yusuf Shitu Galambi
Sanata ya ce babu bayanan kasafin kudin 2024
Malam Ja’afar Ja’afar wanda fitaccen ‘dan jarida ne, yace ya zanta da wani Sanata a majalisar dattawa, kuma ya fada masa irin haka.
Da yake magana a Twitter, Ja’afar Ja’afar ya ce an fada masa babu komai a cikin kwalayen da Bola Tinubu ya gabatar a zauren majalisa.
“Mun zauna jiya domin tattaunawa a kan batun kasafin kudin, amma babu wanda ya samu wata takarda.
Maganar gaskiya shugaban kasa (Bola Tinubu) ya zo ne da kwalaye wayam kurum."
- Inji Sanatan
Karin albashi a kasafin kudin 2024
Gwamnatin tarayya ta ce nan da 'yan watanni kadan sabon tsarin albashi zai soma aiki a tarayya, mafi karancin albashi a yau N30, 000 ne.
Ministan labarai ya ce zuwa Afrilu mafi karancin albashi zai canza. Za a kashe Naira tiriliyan 24 a kasafin 2024, 2025 da na 2026 kan albashin.
Asali: Legit.ng