Kano: Mahaifin Yarinyar da Aka Yi Wa 'Yarsa Kisan Gilla Ya Roki Abba Kabir Bukata 1, Ya Fadi Dalili

Kano: Mahaifin Yarinyar da Aka Yi Wa 'Yarsa Kisan Gilla Ya Roki Abba Kabir Bukata 1, Ya Fadi Dalili

  • Sani Umar ya roki Gwamna Abba Kabir da ya hana sauya kotun da ake shari'ar hallaka 'yarsa da aka yi
  • Sani shi ne mahaifin yarinyar da aka yiwa kisan gilla a shekarar 2019 bayan an yi garkuwa da Ita
  • Ana zargin mata mai suna Fadila Adamu da kisan yarinyar, Aisha Umar wacce ba ta fi shekaru takwas ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Mutumin da aka hallaka masa 'yarsa, Sani Umar ya roki Gwamna Abba Kabir da ya dakatar da dage shari'arsu zuwa wani kotu.

Mahaifin marigayiyar mai suna Aisha Umar da aka mata kisan gilla inda ya ke zargin babban lauyan wadanda ake kara na son sauya wurin shari'ar.

Kara karanta wannan

Bidiyon zanga-zangar da ta barke a Kano kan zargin 'yan sanda sun kashe farar hula

An roki Abba Kabir da ya kawo dauki kan shari'ar wata yarinya da aka yi wa kisan gilla a Kano
An bukaci Abba Kabir ya kawo dauki a shari'ar Aisha da aka yi wa kisan gilla. Hoto: @Kyusufabba.
Asali: Twitter

Mene mahaifin yarinyar ke cewa?

Mallam Umar ya ce dukkan shaidu mutum bakwai sun tabbatar da cewa Fadila Adamu ce ake zargi da aikata kisan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce sauya wurin shari'ar zuwa wani kotun zai dawo da shari'ar farko bayan ci gaban da aka samu, cewar Daily Post.

Mahaifin yarinyar ya kara da cewa kusan dukkan shaidun 'yan uwan Fadila ne wadanda za su iya sauya tunani idan aka sauya wurin shari'ar.

Daily Trust ta tattaro cewa Fadila ta yi garkuwa da Aisha 'yar shekaru 8 a makarantar Islamiyya a shekarar 2019.

Me ake zargin Fadila?

Daga bisani, ta dauke ta inda ta kai ta gidan kanwarta mai suna Shamsiyya Ja'afar inda ta yi kwanaki biyu kafin kai ta gidan wata Aisha Sharu.

Ana zargin Fadila ta kashe yarinyar a kwanaki na hudu yayin da ta jefa ta a rijiya a Unguwar Gandu a Kano.

Kara karanta wannan

Kawu Sumaila: Sanatan NNPP Ya fede gaskiya a shari’ar zaben Gwamnan Jihar Kano

Rundunar 'yan sanda ta yi nasarar kama ta inda ta tabbatar da aikata laifin tare da nuna wa rundunar inda gawar yarinyar ta ke.

Kwamishinan Shari'a a jihar, Barista Haruna Isa ya ce su na bibiyar shari'ar kuma zai tabbatar an yi adalci a shari'ar.

Abba ya kwashe mahaukata a kan tituna

A wani labarin, Gwamn Abba Kabir na jihar Kano ya kwashe dukkan mahaukata da ke yawo kan titunan birnin Kano.

Gwamnan ya dauki wannan matakin ne bayan samun korafe-korafen jama'a kan yadda mahaukatan su ka cika birnin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.