Kano da Gombe: Gwamnati Ta Sallami Fursunoni 332 Daga Gidajen Gyara Hali Kan Dalili 1 Tak

Kano da Gombe: Gwamnati Ta Sallami Fursunoni 332 Daga Gidajen Gyara Hali Kan Dalili 1 Tak

  • Gwamnatin tarayya ta sanar da sallamar fursunoni 332 daga jihohi biyu na Arewacin Najeriya don rage cunkoso a gidajen gyara hali na kasar
  • Daga jihar Kano ministan cikin gida ya sallami fursuononi 150, yayin da babbar jojin jihar Gombe ta sallami fursunoni 182 daga jihar Gombe
  • Wannan na daga cikin shirin gwamnatin Shugaba Tinubu na rage cunkoson fursunoni a gidajen gyara hali na kasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihohin Kano, Gombe - Gwamnatin tarayya ta yi afuwa ga fursunoni 150 da aka kulle su kan laifukan da za a iya biyan tara ko diyya a gidajen gyara hali na jihar Kano, cikin 4,068 da ke fadin kasar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya Za Ta Biya N585m a Shiga Sallamar Wadanda Aka Daure a Kurkuku

Hakan na zuwa yayin da babbar jojin jihar Gombe, mai shari'a Sadiya Mohammed ta sallami fursunoni 182 daga gidajen gyara hali da ke jihar.

Gwamnati ta sallami fursunoni daga jihar Kano da Gombe
Yayin da ministan cikin gida ya sallami fursunoni 150 a jihar Kano, ita kuma babbar joji Sadiya ta sallami 182 a jihar Gombe. Hoto: @CorrectionsNg
Asali: Twitter

Ministan cikin gida, Dr Olubunmi Tunji-Ojo yayin kaddamar da shirin afuwar a babban ofishin hukumar kula da gyaran hali na Kano, ya ce hakan zai rage cinkoso a gidajen gyara hali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Minista ya sallami fursunoni 150 a Kano

Daily Trust ta ruwaito cewa ministan ya samu wakilcin Dr Nzekwe Romanus Anayo daga ma'aikatar, inda ya ce:

"Da yawa daga wadanda aka sallama sun kusa cika wa'adinsu kuma an rufe su ne saboda gaza biyan tarar da aka sanya masu.
"Wasu mutane, kungiyoyi da kamfanoni da ke neman lada ne suka tara naira biliyan 585 domin gudanar da ayyukan taimakon jama'a, inda aka cire akalla naira miliyan 13.5 don fitar da fursunonin na kano."

Kara karanta wannan

"Cin zabe sai an hada da rauhanai" Shehu Sani ya yi wa Doguwa martani

Ya ce wannan shirin na daga cikin kudurorin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na samar da sabuwar Najeriya, inda ya ce an ba fursunonin damar yin sabuwar rayuwa.

Kwanturolan gidajen gyara hali Halliru Nababa ya jinjinawa kokarin ministan kan wannan taimako na daukar dawainiyar fursunonin don su zama 'yan kasa na-gari, Tribune Online ta ruwaito.

Babbar joji ta sallami fursunoni 182 a jihar Gombe

A jihar Gombe kuwa fursunoni 182 suka shaki iskar 'yanci bayan da kwamitin bunkasa shari'ar ta'addanci bisa jagorancin babbar jojin jihar ya sa hannu.

Mai shari'a Halima ta ce an sallami fursunoni 141 daga gidajen gyara hali na Gombe, inda ta ce an sallami fursunoni 55 nan take, sai 105 aka bayar da belinsu, da kuma 22 da aka same su sun tuba tare da canja dabi'unsu.

Kwanturolan gidajen gyara hali na jihar Lawan Idris Gusau, ya jinjinawa kokarin babbar jojin da kuma kwamitinta, na fitar da fursunoni 182 daga gidajen gyara hali na jihar.

Kara karanta wannan

Ministoci 9 sun tashi da kaso mafi tsoka a kasafin kudin naira tiriliyan 27 da Tinubu ya gabatar

Matar aure ta datse igiyar aurenta Na wata shida

A wani labarin, Legit ta ruwaito maku cewa wata mata ta wallafa a shafinta na TikTok dalilin da ya sa ta yanke shawarar datse igiyar aurenta duk da bai wuce wata shida ba.

Matar wacce ba a gano asalin sunanta ba, ta ce ta gaji da fadace-fadacen mijin, inda ta nemi kawarta tazo ta raba ta da gidan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.