Luguden Wuta: An Kashe Yan Bindiga Sama da 50 Yayin da Suka Kai Sabon Hari a Jihar Arewa

Luguden Wuta: An Kashe Yan Bindiga Sama da 50 Yayin da Suka Kai Sabon Hari a Jihar Arewa

  • Yan sanda tare da sojoji, yan banga da mafarauta sun halaka yan bindiga sama da 50 a karamar hukumar Bali ta jihar Taraba
  • Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Abdullahi Usman, ya ce sun samu wannan nasara ne ranar Talata da ta gabata
  • Ya ce jami'an tsaron ba su tsaya iya nan ba, sun baza komarsu a yankin da nufin damƙo sauran yan bindigan da suka tsere

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Taraba - Ƴan bindiga akalla 50 da suka addabi kauyukan ƙaramar hukumar Bali a jihar Taraba, sun gamu da ajalinsu a hannun jami'an tsaro.

Hukumar 'yan sanda reshen jihar Taraba ta tabbatar da wannan nasara ta hannun jami'in hulɗa da jama'a na hukumar, Abdullahi Usman.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun halaka dan bindiga, sun ceto malamin addini da wasu mutum 2 a jihar arewa

Yan sanda da haɗin guiwar jami'an tsaro sun kashe yan bindiga a Taraba.
Yan Sanda: Yan Bindiga Sama da 50 Sun Bakunci Lahira a Jihar Taraba Hoto: PoliceNG
Asali: Twitter

A wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, Usman ya shaida wa Channels tv cewa dakarun 'yan sanda da haɗin guiwar sauran hukumomin tsaro ne suka kashe ƴan bindigan ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka halaka yan ta'addan

Kakakin 'yan sandan ya bayyana cewa jami'an tsaron sun yi kwantan ɓauna tare da kashe 'yan bindigan bayan mazauna yankin sun nemi agajin gaggawa.

A rahoton jaridar Daily Post, Abdullahi Usman ya ce:

"Hukumar 'yan sandan Taraba ta samu rahoton cewa wasu ƴan bindiga da ake zargin masu garkuwa ne sun kai farmaki kauyen Tonti da ke yankin ƙaramar hukumar Bali."
"Yan bindigan sun shiga ƙauyen da karfe 5:30 na safe daidai lokacin da Musulmai ke Sallar Asubahi, daga zuwa kuma suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi."
"Bayan samun rahoton kwamishinan ƴan sanda, Joseph Eribo, ya bada umarnin tura dakaru da haɗin guiwar sojoji, yan banga da mafarauta, wanda daga isa aka fara musayar wuta."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sama da 300 sun kewaye babban birnin jihar arewa, sun kashe jami'an tsaro sama da 20

"Yayin haka ne da yawan yan bindigan suka gamu da ajalinsu saboda luguden wutan jami'an tsaron yayin da sauran suka ari na kare ɗauke da raunukan harbi."

A cewar kakakin 'yan sandan, jami'an tsaro sun bazu ta ko ina a yankin domin kamo sauran ƴan bindigan da uka gudu.

Yan Bindiga Sun Farmaki Motar Kuɗin Gwamnati

A wani rahoton kuma Yan bindiga sun kwace motar kuɗi ta gwamnatin jihar Ogun kuma sun yi awon gaba da makudan kuɗaɗe masu yawa ranar Laraba.

Maharan waɗanda ake zargin ƴan fashi da makamai ne sun kuma kashe hadimin Gwamna Abiodun wande ke biye da kuɗin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262