Ministoci 9 Sun Tashi Da Kaso Mafi Tsoka a Kasafin Kudin Naira Tiriliyan 27 Da Tinubu Ya Gabatar

Ministoci 9 Sun Tashi Da Kaso Mafi Tsoka a Kasafin Kudin Naira Tiriliyan 27 Da Tinubu Ya Gabatar

  • Kundin kasafin kudin da Bola Ahmed Tinubu ya gabatar ya nuna gwamnatin tarayya za ta kashe N27.tr a shekara mai zuwa
  • An ware sama da N3tr domin tsaro da harkokin ‘yan sanda yayin da kasafin kudin Ministan harkar kiwon lafiya ya kai N1.33tr
  • Sauran Ministocin da aka warewa kudi masu yawa a kasafin sun hada da na harkar lantarki, sufuri da kuma Ministan jirage

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Sha’anin tsaro, cigaban al’umma, kiwon lafiya da kuma harkar ilmi aka fi maida hankali a kan su a cikin kasafin kudin 2024.

Rahoton da The Nation ta fitar ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta fi ba wadannan bangarori muhimmanci a kundin kasafin badi.

Tinubu ya fada da bakinsa cewa gwamnatin Najeriya ta bada karfi sosai ga tsaro da zaman lafiya wanda ya ce sai da su ake iya samun cigaba.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba na Kano zai faranta ran tsofaffin ma’aikata, an tsaida ranar fara biyan kudin giratuti

Tinubu da kasafin kudi
Bola Tinubu ya kawo kasafin kudin 2024 Hoto:@PBATMediaCentre
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kasafin 2024 zai taimakawa marasa galihu

Rahoton ya ce gwamnati za ta kashe kudi domin cigaban yara wanda su ne manyan gobe.

Za a fadada tsarin da ake da shi na taimakawa marasa galihu domin kara adadin talakawa da gidajen marasa karfi da za a tallafa rayuwarsu.

Ta ina za a samu kudi a kasafin kudin 2024?

Ganin ana kukan babu kudi a gwamnati, Bola Tinubu ya ce za a gyara dokokin haraji domin ganin gwamnati ta samu isassun kudin shiga.

Yayin da gwamnatin tarayya ta ke ganin za ta tatso N10.8tr wajen kudin shiga, za a samu gibin N9.18tr da za a cike shi ta hanyar cin bashi.

Shugaban kasar ya yi alkawarin toshe kofofin barna da facaka a gwamnati, sannan za a saida wasu kadarori kuma ayi aiki da ‘yan kasuwa.

Kara karanta wannan

Kasafin 2024: Jam'iyyar SDP ta shirya yin aiki da Tinubu don ci gaban Najeriya

Ma’aikatun da su ka samu tiriliyoyi a kasafin 2024

Punch ta ce za ware N50bn domin ba dalibai bashi sannan ma’aikatun tsaro da na harkokin ‘yan sanda kashe N3.25tr a shekarar ta badi.

N1.32tr aka ware domin abubuwan more rayuwa irinsu wuta, sufuri, ruwa, jirage da gidaje, sai kasafin kiwon lafiya ya karu zuwa N1.33tn.

Gwamnati tayi kasafin Naira tiriliyan 27.50

Ana da labari Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kundin kasafin kudin a majalisar tarayya inda ya ce ana sa ran batar da N27.tr.

Ana so a 2024 kason kudin shiga ga karfin tattalin arziki watau GDP ya kai 18% daga 10%.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng