Yan ta’adda sun bindige makanike har lahira, sun tafi da matarsa da yarsa a Nasarawa

Yan ta’adda sun bindige makanike har lahira, sun tafi da matarsa da yarsa a Nasarawa

  • Yan bindiga sun kai kazamin hari yankin Gandu na jami'ar tarayya ta Lafia, jihar Nasarawa
  • Maharan sun halaka wani makanike mai suna Danteni sannan suka sace mata da diyarsa
  • Mummunan al'amarin ya afku ne a ranar Litinin, inda yan bindigar suka yi harbe-harbe don tsorata jama

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Nasarawa - Tsagerun yan bindiga sun farmaki yankin Gandu na jami'ar tarayya ta Lafia a ranar Litinin, inda suka kashe wani makanike, sannan suka yi garkuwa da mata da diyarsa, rahoton LIB.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa maharan sun farmaki garin da misalin karfe 7:00 na yamma sannan suka yi ta harbi kan mai uwa da wahabi domin tsorata mazauna yankin.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace malamin addinin musulunci da amarya da ango a Kaduna

Yan bindiga sun halaka makanike tare da sace mata da diyarsa
Yan ta’adda sun bindige makanike har lahira, sun tafi da matarsa da yarsa a Nasarawa Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

An tattaro cewa marigayin, wanda aka bayyana a matsayin Danteni, ya ji rauni sakamakon harbi kuma ya mutu a asibitin da aka kai shi jinya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa gaba daya dalibai da sauran mazauna yankin duk sun shige cikin gida.

Rundunar yan sanda ta tabbatar da harin

Kakakin yan sandan jihar, DSP Rahman Nansel, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira ta wayar tarho.

Ya ce mutum daya ya mutu a harin yayin da yan bindigar suka yi awon gaba da mata da diyar marigayin.

Har wayau, ya ce rundunar yan sandar ta tura jami'anta zuwa wajen da abun ya faru bayan ta samu kira mai cike da damuwa cewa yan bindiga na ta harbi a yankin Gandu.

Sai dai kuma, ya ce ko da jami'an yan sanda suka isa yankin, sun gano cewa an harbi wani Danteni, makanike. Ya kara da cewar mutumin ya mutu a asibiti.

Kara karanta wannan

Yanzu: Tashin hankali yayin da jami'an NSCDC suka harbi dalibai a Abuja yayin jarrabawa

“Jami’an mu na ’yan sandan sun koma tare da tawagar tsaro don kare al’ummar Gandu baki daya amma kafin su isa gidan marigayin, yan bindigar sun tafi da matarsa.
"Jami'anmu sun kakkabe gaba daya yankin amma duk kokarin da aka yi na ceto matar ya ci tura."

Yan bindiga sun kai farmaki Kaduna

A wani labarin kuma, mun ji cewa wasu yan bindiga sun farmaki al'ummar Dan-Honu da ke Millennium City, karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna inda suka sace sabbin ma'aurata, malamin addinin musulunci da wasu mutane a ranar Talata, 28 ga watan Nuwamba.

An tattaro cewa maharan sun kai hari ne sanye da bakaken kaya da bindigogin AK47 su da yawa da misalin karfe 9:00 na dare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng