CBN Ya Aike da Sabon Umarni Ga Bankuna Kan Amfani da Tsoffi da Sabbin Takardun Naira

CBN Ya Aike da Sabon Umarni Ga Bankuna Kan Amfani da Tsoffi da Sabbin Takardun Naira

  • Bayan hukuncin kotun koli, babban bankun Najeriya (CBN) ya baiwa bankuna sabon umarni kan amfani da tsoffi da sabbin takardun naira
  • CBN ya umarci rassansa na jihohi su baiwa bankuna tsoho da sabon kuɗin daga nan har illa masha Allah
  • A wata sanarwa daga CBN, ya umarci ƴan Najeriya su ci gaba da amfanin kuɗin a harkokin su na yau da kullum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya umarci rassansa na faɗin kasar nan su ci gaba da mu'amala da tsoffi da sabbin takardun naira.

Babban bankin ya umarci su bayar tare da karɓan dukkan takardun naira, tsoffi da sabbi, yayin gudanar da harkoki da bankunan kasuwanci (DMBs).

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun Koli ta yanke hukunci kan dena amfani da tsaffin takardun naira a Najeriya

Takardun naira.
CBN ya umarci bankuna su ci gaba da mu'amala da tsoffi da sabbin naira Hoto: CBN
Asali: Twitter

Wannan umarni na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun CBN, Sidi Ali Hakama, rattaɓa wa hannu kuma aka wallafa a shafin manhajar X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa CBN ya ba da wannan umarnin ne biyo bayan hukuncin kotun ƙoli na halasta amfani da kuɗin har illa masha Allahu.

Sanarwan ta ce:

“Saboda haka, duba da sashi na 20 (5) na dokar CBN 2007, duk takardun kudin da babban bankin Najeriya (CBN) ya fitar, za su ci gaba da zama halastattu a kan doka, har illa masha Allahu."
"Muna kira ga ɗaukin al'umma su ci gaba da karɓan dukkan takardun naira (tsoffi da waɗanda aka sauya wa fasali) a harkokinsu na yau da kullum."
"Kuma su ci gaba da mu'amalarsu da takardun kuɗin cikin kula domin guje wa lalacewar takardun kuɗin."

Kara karanta wannan

Kotu ta yi adalci, ta yanke hukunci kan mutumin da ya daɓawa maƙocinsa wuka har lahira

Babban bankin CBN ya kuma bukaci jama’a da su rungumi wasu hanyoyin mu'amala da kudi, kamar ta intanet, domin rage matsi kan amfani da tsabar takardun kudi.

A ranar Laraba ne kotun koli ta amince da bukatar ministan shari’a kuma Antoni Janar na kasa, Lateef Fagbemi na tsawaita amfani da tsofaffin takardun naira har sai baba ta gani.

Legit Hausa ta tattauta da wasu yan Najeriya kan wannan ci gaban, inda wasu suka ce sun manta da wani wa'adin amfani da tsofaffin kudi da sabbi.

Umar Ibrahim, ɗan asalin jihar Katsina ya ce ya manta an sauya takardun kuɗi kuma tsoffin suna da wa'adi.

"Ni na manta gaskiya amma rannan na yi mamaki da naje cire kuɗi wajen masu POS aka ce mun babu, zaka ga idan kana da N10,000 kaɗan daga ciki ne sabbi, duk tsofaffin muke amfani da su."
"Duk da haka zan iya cewa gwamnati ta yi abinda ya dace, sai dai ba zamu manta wahalar da aka jefa mu ba lokacin canza kuɗin nan," in ji shi.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa, tsohon shugaban lauyoyi sun soki tafka da warwaran Alkalai a shari’ar Kano

Wakilin mu ya garzaya wurin masu POS, inda ya samu tabbacin cewa tsabar kuɗi sun fara ƙaranci. A ɗaya daga cikin inda ya je babu takardun kuɗin.

Bugu da ƙari, Kabir Yahaya, wani mai sana'ar POS a Dabai, jihar Katsina ya yi rangwamen cewa duk wanda ya kawo tsabar kuɗi, za a tura masa a asusu kyauta.

Jami'an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zanga a Kogi

A wani rahoton kuma Jami'an tsaro sun tarwatsa magoya bayan jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a jihar Kogi waɗanda suka ɓarke da zanga-zanga a ofishin INEC.

Magoya bayan SDP sun mamaye babbar hedkwatar INEC da ke Lokoja, babban birnin jihar Kogi domin nuna adawa da abinda suka kira, "maguɗin kayan zaɓe."

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262